'Yan Ta'adda Sun Halaka Mutum 2 a Jihar Katsina a Wani Sabon Hari

'Yan Ta'adda Sun Halaka Mutum 2 a Jihar Katsina a Wani Sabon Hari

  • Rayukan wasu bayin Allah mutum biyu sun salwanta bayan ƴan ta'adda sun kai sabon farmaki a ƙaramar hukumar Dandume ta Katsina
  • Miyagun ƴan ta'addan sun kuma tasa ƙeyar mutane masu yawa zuwa cikin daji a sabon harin da suka kai cikin dare
  • Mutanen yankin sun miƙa ƙoƙon bararsu ga gwamnatin jihar domin kawo musu ɗaukin gaggawa daga hare-haren ƴan ta'addan

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Katsina - Ƴan ta'adda da ke a dazukan ƙaramar hukumar Dandume a jihar Katsina, sun halaka mutum biyu a wani sabon hari da suka kai.

Mutanen biyu da ƴan ta'addan suka halaka dai akwai mace ɗaya da namiji ɗaya, sannan suka yi awon gaba da mutane masu a farmakin da suka kai.

Yan ta'adda sun halaka mutum biyu a Katsina
'Yan ta'addan sun shiga garin ne da daddare Hoto: Theguardian.com
Asali: UGC

Wani majiya ya gayawa jaridar ait.live cewa lamarin ya auku ne ranar Lahadi, 13 ga watan Agusta, da daddare wajen misalin ƙarfe 8:00 bayan kammala Sallar Isha'i.

Kara karanta wannan

Jami'an Hukumar Kwastam Sun Kama Harsasai 1,245 Da Aka Boye Cikin Buhunan Shinkafa 'Yar Waje

A cewarsa ƴan ta'addan sun shigo ne ta hanyar da ke zuwa maƙabarta kusa da gidan wani Rabiu Mai Atamfa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jama'a na cikin fargaba kan harin ƴan ta'adda

Majiyar ya ƙara da cewa mutanen yankin yanzu sun koma rayuwa cikin tsoro saboda fargabar harin ƴan ta'adda inda ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta taimaka ta kawo musu ɗauki.

Rundunar ƴan sanda jihar Katsina har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton ba ta ce komai ba dangane da sabon harin da ƴan bindigan suka kai.

Idan ba a manta ba dai, a cikin ƴan kwanakin nan gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya shirya gudanar da addu'a ta musamman domin samun zaman lafiya a jihar, inda ya sha alwashin ba zai tattauna da ƴan ta'adda ba, a maimakon hakan zai yaƙe su ne ba tare da sassauci ba.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Tashin Hankali Yayin Da 'Yan Bindiga a Wata Jiha Suka Kona Fadar Babban Basarake

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani mazaunin garin na Dandume, mai suna Malam Shamsu wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Malam Shamsu ya bayyana cewa ƴan ta'addan sun kawo farmakin ne a unguwar ƴan Barkono kusa da tsohuwar maƙabarta, lokacin da wasu ke gudanar da Sallar Isha'i.

Ya bayyana cewa ƴan ta'addan na zuwa sai suka buɗe wuta suka kama harbe-harbe, inda suka halaka wani mutum tare da matarsa da ɗansu guda ɗaya.

Ya bayyana cewa an harbi wani mutum ɗaya a ƙafa yayin da wasu suka samu raunika inda ake lafiyarsu a asibiti.

Ya tabbatar da cewa ba a san adadin yawan mutanen da ƴan ta'addan suka sace ba a lokacin harin da suka kawo.

Yan Bindiga Sun Sace Dan Sarki a Zamfara

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun yi awon gaba da ɗan sarkin Bungudu a wani sabon hari da suka kai a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Gwara Haka: Dakarun Sojoji Sun Soye 'Yan Ta'adda Masu Yawa a Arewacin Najeriya a Wani Luguden Wuta Da Suka Yi Musu

Ƴan ta'addan waɗanda su ke ɗauke da manyan makamai sun kuma yi awon gaba da mutum bakwai a harin da suka kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng