NEMA Ta Zayyano Jihohin Najeriya 19 Da Za Su Fuskanci Kalubalen Ambaliyar Ruwa Kwanan Nan

NEMA Ta Zayyano Jihohin Najeriya 19 Da Za Su Fuskanci Kalubalen Ambaliyar Ruwa Kwanan Nan

  • Hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA), ta ba da rahoto kan ambaliyar ruwan da za a samu cikin kwanakin nan
  • Hukumar ta ce aƙalla jihohi 19 ne ke fuskantar barazanar samun ambaliyar ruwa a wata Agusta da muke ciki
  • Kodinetan hukumar na jihar Legas, Mista Ibrahim Farinloye ne ya bayyana hakan yau Litinin

Legas - Hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA), ta bayyana cewa aƙalla jihohin Najeriya 19 ne za su fuskanci mamakon ruwan sama da zai iya janyo musu ambaliyar ruwa.

Kodinetan hukumar na jihar Legas, Ibrahim Farinloye ne ya bayyana hakan ranar Litinin kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta wallafa.

Ambaliyar ruwa jihohin Najeriya
NEMA ta ce jihohi 19 ne za su fuskanci ambaliyar ruwa cikin kwanakin nan. Hoto: Daily Nigerian
Asali: UGC

Jihohi 19 da za su fuskanci ambaliyar ruwa

Jihohin da Mista Farinloye ya lissafo da za su fuskanci ambaliyar ruwan saman sun haɗa da Delta, Ekiti, Ondo, Legas, Anambra, Ogun da jihar Nasarawa.

Kara karanta wannan

Firaministan Nijar Ya Fadi Abinda Za Su Yi Dangane Da Takunkumin Da ECOWAS Ta Sanya Mu Su

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Karin jihohin da aka bayyana za su fuskanci ambaliyar ruwan su ne Kuros Riba, Bauchi, Jigawa, Osun da kuma jihar Kwara.

Sauran jihohin Najeriya da Farinloye ya ambata sunansu su ne Zamfara, Sokoto, Adamawa, Taraba, Benuwai, Imo, da kuma jihar Abia.

Mutane sun maƙale yayin da ambaliya ta shanye gidaje a Abuja

A baya Legit.ng ta kawo wani rahoto kan wata ambaliyar ruwa da aka samu a rukunin gidaje na Trade Moore, wacce ta yi sanadiyyar maƙalewar mutane da dama.

Ambaliyar wacce ta janyo sanadin rasa rai, ta samo asali ne daga mamakon ruwan da aka yi a cikin babban birnin na tarayya wato Abuja.

Jami'an hukumar NEMA da na hukumar 'yan kwana-kwana sun isa yankin da lamarin ya faru cikin gaggawa, tare da samun nasarar ceto wasu mutanen da abin ya rutsa da su.

Kara karanta wannan

Kyau Ya Hadu Da Kyau: Diyar Biloniya Indimi Ta Amarce Da Babban Dan Kasuwar Kasar Turkiyya

Ruwan sama ya lalata sama da gidaje 100 a jihar Kebbi

Legit.ng a baya ta yi wani rahoto kan sama da gidaje 100 da ruwan sama mai haɗe da iska ya lalata a jihar Kebbi.

Haka nan kuma ruwan ya janyowa mutanen yankin da lamarin ya faru asarar dukiya mai dumbin yawa.

Gwamnatin jihar ta jajantawa mutanen da lamarin ya shafa, tare da alƙawarin ba su gudummawa domin gyara muhallansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng