Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya yi barna a jihar Katsina, 25 sun mutu

Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya yi barna a jihar Katsina, 25 sun mutu

Ruwan sama kamar da bakin kwarya ta janyo dimbin asara a karamar hukumar Jibi ta jihar Katsina, inda kimanin mutane ashirin da biyar, 25, suka rigamu gidan gaskiya a sakamakon ambaliyan ruwan, tare da lalata akalla gidan Casa’in, 90.

Jaridar This Day ta ruwaito baya ga asarar rayuka da gidaje, sama da tumaki dari biyu da sittin ne ruwan ya halaka, tare da dukiyoi na miliyoyin nairori, da suka hada da motoci, babura da gonakai da dama, a ranar Litinin, 16 ga watan Yuli.

KU KARANTA:

Majiyar Legit.ng ta ruwaito daga cikin garuruwan da barnar ya shafa akwai Kwata, Dantudu, Sabuwar Tukare, Tsohuwar Tukare, Unguwar mai Kwari, inda rahotanni suka nuna cewar da misalin karfe 11 na dare aka fara ruwan, kuma ya tsaya da karfe 1 na dare.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya yi barna a jihar Katsina, 25 sun mutu
Ambaliya

Bugu da karo bincike ya nuna daga cikin mutane 25 da suka mutu a sanadiyyar karfin ruwan, akwai wata mata mai siyar da abinci da yayant guda biyu, wanda ruwan ya tafi da shagon siyar da abincinsu dungurungum yayin da suke cikin shagon.

Majiyarmu ta gana da Hakimin Jibia, Alhaji Rabe Rabiu, wanda ya bayyana lamarin a matsayin mummunan lamari da ya jefa al’ummar garin Jibia cikin mawuyacin hali, yace:

“Mun gano gawarwaki 25, sa’annan wasu kuma sun bace, sama da shanu, akuya da raguna 260 sun bace.” Daga karshe Rabe ya yi kira ga gwamnatocin jiha na tarayya da su kai musu dauki don kuwa matsalar ta fi karfinsu.

Shima a nasa bangare, jami’in watsa labaru na karamar hukumar Jibia, Sa’ad Suleiman ya bayyana matakan da suke dauka wajen magance ambaliyar ruwa da suka hada da yashe kwatoci, yashe tekuna tare da yin kira ga jama’a dasu daina zuba bola a magudanar ruwa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel