SERAP Ta Maka Akpabio, Abbas A Kotu Kan Naira Biliyan 110 Na Motocin Alfarma Da Tallafin Sabbin Mambobi

SERAP Ta Maka Akpabio, Abbas A Kotu Kan Naira Biliyan 110 Na Motocin Alfarma Da Tallafin Sabbin Mambobi

  • Hukumar SERAP ta maka shugabannin majalisun Tarayya, Godswill Akpabio da Tajudden Abbas kan kashe Naira biliyan 110
  • Majalisun sun ware Naira biliyan 40 na motocin alfarma da biliyan 70 na tallafi ga sabbin mambobinsu
  • SERAP ta bukaci babbar kotun Tarayya da ke jihar Legas ta hana Akpabio da Abbas amfani da wadannan kudade

FCT, Abuja – Hukumar Kare Hakki da Tabbatar da Gaskiya (SERAP) ta maka shugaban majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da kakakin majalisar Wakilai, Tajudden Abbas kan Naira biliyan 110 na motoci da tallafi.

Majalisun guda biyu za su kashe Naira biliyan 40 don siyan motocin alfarma guda 465 da kuma biliyan 70 na tallafi ga sabbin mambobin majalisun.

SERAP ta maka Akpabio, Abbas a kotun kan Naira biliyan 110 na motocin alfarma
Hukumar SERAP Ta Maka Akpabio Da Abbas A Kotu Kan Naira Biliyan 110. Hoto: Godswill Akpabio/Tajudden Abbas.
Asali: Facebook

SERAP ta sanar da shigar da shugabannin majalisar kotu ne bayan Godswill Akpabio ya ce majalisar ta tura kudaden shakatawa na hutu ga mambobin majalisar yayin da ‘yan Najeriya ke cikin kunci.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Malaman Izala sun dira Nijar don neman hanyar sulhu a batun juyin mulki

A ina SERAP ke karar Akpabio, Abbas?

Babbar kotun Tarayya da ke jihar Legas ta karbi korafin SERAP inda ta bukaci kotun ta umarci Akpabio da Abbas su yi gyara tare da rage wadannan kudade ga mambobi da kuma shugabannin majalisun, cewar Vanguard.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

SERAP ta kuma bukaci a dakatar da Apkabio da Abbas kan kashe kudaden har sai an samar da mafita ga miliyoyin mutane da ke cikin talauci a kasar wanda akalla sun kai miliyan 137.

Ta kuma bukaci a umarci tare da tilasta Mista Akpabio da Mista Abbas da su rage yawan kasafin majalisar zuwa Naira biliyan 110 don samun daidaito da halin da kasar ke ciki na matsin tattalin arziki, cewar Channels TV.

Ta ce:

“’Yan Najeriya suna da damar sanin gaskiyar abin da ke tafiya da kuma samun bayanai na kokarin da jagororinsu ke yi da suka hada da ‘yan majalisu da suke da hakki a kansu.”

Kara karanta wannan

Gwamnan CBN Ya Fadi Abin Da Ya Jawo Naira Ta Sunkuya War-Was a Kasuwar Canji

Me lauyoyin SERAP suka ce?

SERAP ta kara da cewa:

"Yayin da aka ware Naira biliyan 70 na tallafin sabbin mambobi 306, Naira biliyan 500 kacal aka warewa talakawa miliyan 12.
"Sannan an ware Naira biliyan 40 don siyan motocin alfarma 465 ga mambobi da kuma shugabannin majalisun."

Lauyoyin SERAP, Kolawole Oluwadare da Blessing Ogwuche sun bayyana cewa hakan ya tauye hakkin 'yan Najeriya kamar yadda kundin tsarin mulki ya tabbatar.

Akpabio Ya Yi Katobara Kan Tura Musu Kudin Hutu

A wani labarin, shugaban majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya yi katobara yayin zaman majalisar na karshe a makon da ya gabata.

Akpabio cikin kuskure ya ce an tura musu kudade asusun bankunansu don more hutun da suke shirin tafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.