"Ka Juya, Ba Na Gida": Martanin Davido Ga Masoyinsa Da Ya Taho Daga Benue Zuwa Legas a Keke Don Ganawa Da Shi

"Ka Juya, Ba Na Gida": Martanin Davido Ga Masoyinsa Da Ya Taho Daga Benue Zuwa Legas a Keke Don Ganawa Da Shi

  • Martanin da fitaccen mawaƙi Davido ya yi wa wani masoyinsa ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumunta
  • Davido ya samu labarin cewa wani ya taho daga Benue zuwa Legas a keke domin ganawa da shi, inda take ya nemi ya juya
  • Martanin da mawaƙin ya yi ya ja hankulan masu amfani da kafafen sada zumunta, waɗanda suka bayyana ra'ayoyinsu

Martanin da fitaccen mawaƙin nan David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido ya yi wa wani masoyinsa da ya taho daga Benue zuwa Legas a keke ya janyo muhawara a Intanet.

Wani mai amfani da kafar Twitter mai suna @Ssbmuzik ne ya wallafa hotunan wani mai suna @emmiwuks, wanda ya ce ya taho daga jihar Benue zuwa Legas domin haɗuwa da mawaƙin.

Kara karanta wannan

Fitaccen Jarumin Fim Din Kannywood Ya Gamu Da Babbar Jarabawa, Ya Nemi a Taimaka Ma Sa

An yi muhawara kan martanin da Davido ya yi wa masoyinsa
Martanin Davido kan masoyinsa da ya hawo keke zuwa Legas ya janyo muhawara. Hoto: @davido, @emmiwuks
Asali: Twitter

Martanin Davido kan masoyin na sa da ya taho a keke

@Emmiwuks ya bayyana cewa matashin ya shafe kwanaki takwas a kan tafiyar da ya fara domin haɗuwa da mawaƙin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An ga mutumin ɗauke da hoton mawaƙi Davido da kuma wani rubutu da ke cewa “daga Benue zuwa Legas domin Davido.”

Jim kaɗan bayan ganin yunƙurin da matashin ya yi, Davido ya yi gaggawar yin martani, inda ya faɗa ma sa cewa ya juya domin baya gida.

Martanin masu amfani da kafafen sada zumunta kan kalaman na Davido

Kalaman da mawaƙin ya yi wa masoyin na sa da ya taho daga Benue zuwa Legas domin haɗuwa da shi ya janyo muhawara a Intanet.

Ga abinda wasu ke cewa:

smilingapez ya ce:

“Ta ya ka ke tunanin samun mutumin da ya yi waƙar ‘ba na nan’ a gida.”

Kara karanta wannan

‘Yadda Cire Tallafin Man Fetur Ya Tunzura Ni Aikata Fashi Da Makami’, Direba Ya Yi Bayani

danyfundz_ ya ce:

“Bai saurari sabuwar waƙar nan ba ne ta ‘ba na nan’ ??”

Big___khalifa ya ce:

“Davido ya ce ka juya kawai, wannan karon ba zai yi rabon kuɗi ba.”

suaveskin.co ya ce:

“Za ka ziyarci mutum amma ba ka faɗa ma sa ba. Shin Davido mata ce da ka ke son aura da za ka yi wa ziyarar bazata?”

Ogomimi22 ya ce:

“Ka yi tunanin lokacin da ya yi waƙar ‘ba na nan’ da wasa yake?”

Matasan Maiduguri sun ƙona hotunan Davido

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan ƙona hotunan mawaƙi Davido da wasu matasa suka yi a birnin Maiduguri na jihar Borno.

Matasan sun yi hakan ne biyo bayan wani faifan bidiyo na izgili ga addinin Musulunci da mawaƙin ya wallafa a shafinsa na kafar sada zumunta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel