Orire Agbaje: Budurwar da ke Jami’ar UI da ta Samu Mukamin Kwamiti a Mulkin Tinubu

Orire Agbaje: Budurwar da ke Jami’ar UI da ta Samu Mukamin Kwamiti a Mulkin Tinubu

  • Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da kwamitin da zai yi aikin gyara tsarin haraji da tattalin arzikin kasa
  • Yayin da kwamitin zai fara aikin watanni biyu, Orire Agbaje ce ta zama babban abin magana a Najeriya
  • Wannan Baiwar Allah ta na karatu a jami’a, amma kokarin ta ya jawo mata samun wuri a kwamitin

Abuja - A ranar Talata, Bola Ahmed Tinubu ya kafa kwamitin da zai kawo gyara ta fuskar haraji da farfado da tattalin arzikin kasar nan.

Abin da ya fi daukar hankalin mutane shi ne ganin Orire Agbaje ta shiga cikin wannan kwamiti da ya tattara kwararru da masana.

Orire Agbaje kuwa, daliba ce da ke karatu a jami’ar Ibadan da ke jihar Oyo. Wannan budurwa ta na karantar ilmin tattalin arziki ne a UI.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Cusa 'Yar 400L a Jami'a a Kwamitin Gyaran Tattalin Arzikin Najeriya

Orire Agbaje
Bola Tinubu tare da Orire Agbaje Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

Orire Agbaje ta shiga kwamiti

Kamar yadda fadar shugaban kasa ta fitar da sanarwa, Agbaje ta na aji hudu ne a jami’a.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Duk da sai a shekarar nan za ta kammala karatun digirinta na farko, dalibar ta samu damar zama kafada da kafada da masana tattalin arziki.

Tashar Channels ta tabbatar da cewa dalibar ta na cikin gidauniyar NHEF ta masana daga cikin wadanda su ke karatun gaba da sakandare.

Baya ga haka, Agbaje ta na rike da shugabancin kungiyoyi biyu a wannan tsohuwar jami’a mai dinbin tarihi; UI Tax Club da SEIHUnibadan.

Orire Agbaje: Sanarwar fadar shugaban kasa

"Daya daga cikin ‘yan kwamitin tattalin arziki da yi wa haraji garambawul da shugaban kasa @officialABAT ya kaddamar a yau ita ce Miss Orire Agbaje
Dalibar ilmin tattalin arziki ce a jami’ar Ibadan wanda ta ke aji hudu, kuma it ace shugabar kungiyar @ui_taxclub, @SEIHUnibadan kuma ‘yar NHEF."

Kara karanta wannan

Ministocin Tinubu: Majalisa Ba Ta Tabbatar da El-Rufa'i Ba, Ta Amince da Mutum 45

- Fadar shugaban kasa

Shafin Agbaje a LinkedIn

Da Legit.ng Hausa ta duba shafinta, an fahimci ba a banza Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dauko ta ba domin kuwa ta san kan aikinta.

Yanzu haka ni daliba ce mai karatun digirin farko a Jami’ar Ibadan, ina karantar ilmin tattalin arziki
Na maida hankali kan tsare-tsaren kudi da kuma manfufofin tattalin arzikin kasashen Duniya.
Sha’awar harkar kudi ta jawo na yi jarrabawa ICAN kuma na samu ido a bangaren tattalin arziki da haraji da na ke samun ilmi a kai.

Baya ga sha’anin boko, Agbaje ta kan yi ayyukan sa-kai domin samun gogewa. Dalibar ta bayyana kan ta a matsayin wanda ta iya aiki da jama’a.

A yammacin Talata aka ji ta na yi wa shugaban kasa godiya na wannan dama da ya ba ta.

Nadin Ministocin Tinubu

Zuwa yanzu ku na da labari babu sunayen Nasir El-Rufai da Sanata Sani Danladi a jerin Ministocin da ‘Yan Majalisa su ka amince da su.

Duk da kokarin da tsohon Gwamnan ya yi a Majalisa, bai samu shiga ba tukuna, ana jiran rahoton jami'an tsaro a kan su tare da Stella Okotete.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng