An yi wa Arewa Sakayya da Rabon Mukamai a Mulkin Tinubu - Mai Bada Shawara

An yi wa Arewa Sakayya da Rabon Mukamai a Mulkin Tinubu - Mai Bada Shawara

  • Abdulaziz Abdulaziz ya ce Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu tayi wa mutanen Arewa riga da wando
  • Mai taimakawa shugaban Najeriya ya kawo yadda shugaban kasa ya warewa yankinsa tulin mukamai
  • Kwararren ‘dan jaridar yake cewa daga wajen rabon Ministoci za a fahimci gatan da aka yi wa Arewa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Abdulaziz Abdulaziz shi ne Mai taimakawa shugaban Najeriya wajen harkokin jarida, ya yaba da tafiyar Mai gidansa, Bola Ahmed Tinubu.

Da yake magana a Facebook kwanan nan, Malam Abdulaziz Abdulaziz ya ce mutanen Arewacin Najeriya sun samu mukamai a gwamnatin tarayya.

Hadimin da ya fito daga Kano, ya yi wa rubutunsa take da ‘Bola Tinubu: AREWA SAI GODIYA’

Bola Tinubu
'Yan Arewa sun zabi Bola Tinubu a 2023 Hoto: @AjuriNgelale
Asali: Twitter

Tinubu: Arewa ta fi kowa kujeru a FEC

‘Dan jaridar yayi magana ne da aka kammala tantance Ministoci, yake cewa idan aka duba jerin mutanen da za a nada, ‘Yan Arewa sun fi owa rinjaye.

Kara karanta wannan

Ngozi Okonjo-Iweala: Abin da Mu ka Tattauna da Shugaban kasa Tinubu a Aso Rock

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abdulaziz ya ke cewa daga yankin Arewa maso yamma an dauko Ministoci 10, sai aka samu 8 daga Arewa ta gabas, haka zalika Arewa ta tsakiya.

Tinubu ya dauko Hafsun tsaro da sauran mukamai

A sojoji, Mai ba shugaban Najeriyan shawara ya ce an dauko wasu shugabannin sojoji daga yankin baya ga Darektan DSS da mutumin Kano ne.

A cewarsa, yankinsu ya tsira da shugaban NIA da na hukumomi masu tsoka kamar NNPC, baya ga SGF da wasu manyan mukarraban shugaban kasa.

Arewa sai godiya a mulkin Tinubu

"AlhamdulilLahi ya zuwa yanzu a ɓangaren ɗane-ɗanen muƙaman gwamnati Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna bai manta da kara da halarcin da mutanenmu na Arewa suka yi masa ba a lokacin zaɓe.
"A cikin kammalallen list na sunayen ministoci ƙididdiga ta nuna cewa Arewa ke da kaso mafi rinjaye (guda 26) a cikin sunayen mutane 47 da za a naɗa ministoci.

Kara karanta wannan

Ku Yi Hakuri: Shugabannin 'Yan Bindiga a Arewa Sun Nemi Afuwa, Za Su Ajiye Makamai

"Arewa-maso-Yamma ita tafi ko ina yawan ministoci (10) domin kuwa shugaban ƙasa ya bada ministoci bibiyu daga jihohin Katsina, Kano da Kebbi. Arewa-maso-Gabas tana da 8 sai Arewa ta tsakiya da take da takwas ita ma.
"Fatanmu shi ne Allah ya sa waɗannan mutane bada kyakkyawan wakilci tare da riƙewa shugaban ƙasa amanar jama'a.
"Ba ya ga ministoci shugaban ƙasa ya naɗa ko kuma ya cigaba da aiki da waɗannan ƴan Arewa a manyan muƙamai:
"1. SGF
"2. NSA
"3. CDS
"4. CAS
"5. DG DSS
"6. DG NIA
"7. GMD NNPC
"Da sauran wasu da dama da suka haɗa da SA da manyan mataimaka (SSAs).
"Ko yanzu shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba maras ɗa kunya. Su kuma waɗannan manyan jami'ai Allah ya sa kada su bawa shugaban ƙasa da al'ummar mu kunya. Amin!"

- Abdulaziz Abdulaziz

Ta leko ta komawa Maryam Shetty

Da farko an ji ya na cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi masu komai a jihar Kano. Ga wakilcin ƴan siyasa, ga kuma na matasa.

Daga baya sai aka ji an cire sunan Maryam Shetty, Dr. Mariya Mahmood Bunkure ta samu goyon bayan Sanatoci, za ta zama Minista a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng