Abba Gida Gida Ya Yi Sababbin Nade-Naden Mukamai 15 a Jihar Kano
- A farkon makon Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin shugabannin hukumomin gwamnatin Kano
- Mai girma Gwamnan jihar Kano ya fitar da sanarwa ta ofishin Babban sakataren yada labaransa a dazu
- Sanusi Dawakin Tofa ya ce a wadanda aka ba mukamai akwai Dr. Indabawa da Dr. Abubakar Minjibir
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Kano - A ranar Litinin, 7 ga watan Agusta 2023, Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da nadin wasu shugabannn hukumomin gwamnatin jihar Kano.
Sakataren yada labarai na gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya bada sanarwar a wani jawabi na musamman da ya fitar a shafinsa.
Nade-naden shugabannin da aka yi ya kunshi hukumomin kula da alkaluma da cibiyar koyon kasuwanci ta Aliko Dangote da wasu makarantu.
Farfesa Aliyu Isa Aliyu ya samu matsayi
Farfesa Aliyu Isa Aliyu wanda malamin lissafi ne a jami’ar tarayya ta Dutse ya samu matsayi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jerin mukaman da aka raba
1. Hon. Kabiru Getso Haruna – Babban shugaban hukumar tallafawa dalibai.
2. Farfesa Aliyu Isa Aliyu – Darekta Janar na hukumar alkaluma ta Kano.
3. Dr. Kabiru Ado Zakirai – Babban shugaban hukumar kula da makarantun sakandare (KSSMB)
4. Hon. Alkasim Hussain Wudil – Shugaban cibiyar koyon sana’a ta Aliko Dangote
5. Farouq Abdu Sumaila – Shugaban hukumar jagoranci da bada shawara.
6. Alh. Umar Shehu Minjibir - Shugaban hukumar kula da aikin gwamnati a Kano.
7. CP Kabiru Muhammad Gwarzo mai ritaya – Darekta Janar na cibiyar tsaro, Gabasawa.
8. Dr. Abdullahi Garba Ali – Darektan makarantar Informatics, Kura.
9. Hajia Shema'u Aliyu – Darekta cibiyar harkar tarbar baki.
10. Dr. Musa Sa'ad Muhammad- Darektan cibiyar wasanni, Karfi.
11. Dr. Abubakar Shehu Minjibir – Darektan cibiyar cigaban aikin jarida.
12. Abdullahi S. Abdulkadir – Darektan cibiyar aikin gonawa, Kadawa.
13. Jazuli Muhammad Bichi – Darektan cibiyar dabbobi, Gargai.
14. Dr. Maigari Indabawa – Darektan cibiyar harkar fina-finai, Tiga.
15. Kabiru Yusuf – Darektan cibiyar harkar kifi, Bagauda.
Sanarwar ta ce duka wadanda aka nada za su karbi ragamar aiki nan da sa’o’i 48. Abin da hakan yake nufi shi ne za su shiga ofis zuwa ranar Laraba.
Gwamna ya fito da karin Hadimai
A wata sanarwar dabam, an ji Mai girma Gwamnan ya kara nada wasu masu bada shawara:
1. Hon. Garba Dirbunde
2. Hon. Wakili Aliyu Garko
3. Air Commodore Yusha'u Salisu Tudunwada Wada mai ritaya
4. Hon. Musa Ado Tsamiya
5. Gwani Musa Falaki
6. Dr. Sulaiman Wali Sani Mni,
7. Farfesa Auwalu Arzai
8. Hon. Ahmad Sawaba
9. Alh. Tajuddeen Gambo
10. Hon. Baba Abubakar Umar
Hadiman za su rika ba Gwamna shawara a kan harkokin ilmi, makarantun ‘yan kasuwa, tsaro, lambatu, harkokin addini da kula da gandun jeji.
Abdullahi Umar Ganduje ya kama aiki
Idan aka koma siyasar kasa, za a ji labari ‘yan PDP za su rude da Abdullahi Umar Ganduje ya yi zama da Sanata Anyim Pius Anyim a garin Abuja.
Jigon na PDP kuma tsohon sakataren gwamnatin tarayya ya ziyarci shugaban jam’iyyar APC a jiya, hakan ya kara jawo rade-radin sauya-sheka.
Asali: Legit.ng