Hukumar NYSC Ta Musanta Rade-radin Tura Masu Bautar Kasa Nijar Don Taimaka Wa Sojoji

Hukumar NYSC Ta Musanta Rade-radin Tura Masu Bautar Kasa Nijar Don Taimaka Wa Sojoji

  • Hukumar NYSC ta yi fatali da rade-radin da ake yadawa cewa za ta tura matasa masu bautar kasa zuwa Nijar don taimaka wa a yaki
  • Daraktan hulda da jama'a na hukumar, Mista Eddy Megwa shi ya bayyana haka a Abuja a ranar Asabar 5 ga watan Agusta
  • Wannan na zuwa ne bayan yada wani faifan bidiyo a kafafen sadarwa cewa hukumar na shirin tura matasan zuwa Jamhuriyar Nijar

FCT, Abuja - Hukumar Matasa Masu Yi Wa Kasa Hidima (NYSC) ta musanta jita-jitar da ake yadawa cewa za ta tura masu bautar kasa zuwa Nijar don taimaka wa sojoji.

Daraktan hulda da jama'a na hukumar, Mista Eddy Megwa shi ya bayyana haka a ranar Asabar 5 ga watan Agusta a Abuja.

NYSC ta musanta cewa ta na shirin tura matasa masu bautar kasa zuwa Nijar
Hukumar NYSC Ta Yi Martani Kan Tura Matasa Masu Bautar Kasa Nijar. Hoto: NYSC.
Asali: UGC

NYSC ta yi fatali da rade-radin inda ta ce babu kanshin gaskiya

Kara karanta wannan

Juyin Mulki: Dalilin Da Ya Sanya Yakamata Najeriya Ta Sake Dawo Da Doka Da Oda a Nijar, Reno Omokri Ya Bayyana

Sanarwar na zuwa ne bayan yada wani faifan bidiyo da aka yi a kafafen sada zumunta cewa za ta tura masu bautar kasa zuwa Nijar don yin yaki, PM News ta tattaro.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce:

"Hukumar NYSC na sanar da ku cewa babu kanshin gaskiya a bidiyon da wani mai barkwanci ke yadawa."

Megwa ya ba wa iyalan matasan da sauran mutane hakuri

Ya kara da cewa kamar yadda New Telegraph ta tattaro:

"Mutane da matasa masu bautar kasa da iyalansu duk su yi watsi da wannan labari da ke dauke da karairayi.
"Duk wasu masu barkwanci an shawarce su da su guji yada jita-jita da ke kawo cikas ga zaman lafiyar kasar."

Megwa ya ce hukumar za ta yi iya bakin kokarinta don ganin ta kamo wadanda suka yada wannan labari don su girbi abinda su ka shuka, cewar Leadership.

Kara karanta wannan

Shikenan: Sanatocin Najeriya sun yi maganar karshe kan batun tura sojojin Najeriya su yaki na Nijar

Bai Kamata Shirin NYSC Ya Zama Wajibi Ba, Farfesa Jega Ya Magantu

A wani labarin, tsohon shugaban hukumar zabe, INEC, Farfesa Attahiru Jega ya ce bai kamata shirin NYSC ya zama wajibi ba.

Jega ya bayyana haka ne yayin bikin cikar hukumar shekaru 50 da kafuwa a babban birnin Tarayya, Abuja.

Ya ce a yanzu idan har akwai aikin da ya kamata ya zama dole, sai dai aikin soja kadai a kasar amma ba bautar kasa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.