Tashin Hankali Yayin Da Wasu Suka Hallaka Hadimin Sanata a Jihar Legas

Tashin Hankali Yayin Da Wasu Suka Hallaka Hadimin Sanata a Jihar Legas

  • Yayin da ake ci gaba da nade-nade a kasar nan, Allah ya yi wa dan siyasa a Najeriya rasuwa a jihar Legas
  • Rahoton da muke samu ya ce, an hallaka hadimin Sanata Solomon Adeola na Jihar Ogun a wani yanki na jihar Legas
  • Ya zuwa yanzu, ba a gano gaskiyar abin da ya faru ba, amma an tsinci gawarsa a wani wurin da lamarin ya faru

Jihar Legas - An hallaka Mista Adeniyi Sanni, mai taimakawa Sanata Solomon Adeola na jihar Ogun da ke Kudu maso Yammacin Najeriya.

An hallaka Sanni ne a wani yanayi mai cike da sarkakiya da sanyin safiyar Asabar 5 ga watan Agustan 2023, Daily Trust ta ruwaito.

An tsayar da marigayin ne a wani shingen bincike da ke Legas inda aka ce an yi masa tambayoyi kan takardun motar da yake tukawa.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Najeriya za ta shaida zanga-zangar likitoci da ba a taba gani ba, an fadi yaushe

An kashe na kusa da sanata a Legas
An kashe na kusa da Sanata Solomon Adeola a Legas | Hoto: Senator Solomon Olamilekan Adeola, FCA
Asali: Facebook

Yadda lamarin ya faru

Bayan magana da matarsa a wannan yanayi na dan wani lokaci, daga nan ne ta rasa sadarwa tsakaninsu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Rahotanni sun ce an tsinci gawarsa ne da harbin bindiga a jikinsa sa’o’i kadan bayan haka abin da ya faru, rahoton TheCable.

Mai Sanata Adeola shawara kan harkokin yada labarai, Cif Kayode Odunaro, ya tabbatar da wannan mummunan labarin a wata sanarwa da ya fitar.

Martanin 'yan sanda

Har yanzu dai 'yan sandan ba su mayar da martani ga labarin ba, duk da kira da sakwannin waya da aka tura musu.

Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a Legas, Benjamin Hundeyin, bai amsa tambayoyin da aka tura nasa masa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Ba wannan ne karon farko da ake yiwa 'yan siyasa da makusantansu kisan gilla ba a Najeriya, hakan ya sha faruwa.

Kara karanta wannan

Kitimurmura: Ministan Tinubu ya roki gafarar Sanatoci bayan kiransu wawaye a 2021

A lokuta da dama, akan yi zargin 'yan adawa da kisa irin wadannan kashe-kashe da basu da ma'ana.

Yadda aka farmaki sanata

A wani labarin, 'yan bindiga sun budewa tawagar motocin Sanata Ifeanyi Ubah wuta a garin Enugwu-Ukwu dake karamar hukumar Njikoka dake jihar Anambra ranar Lahadi.

Bidiyon da aka dauka bayan harin ya nuna cewa ana hasashen kimanin yan sandan shida aka kashe a musayar wutar, rahoton SaharaReporters.

A cewar masu idanuwan shaida, wasu yan batagari ne suka budewa mototcin Sanatan wuta ba zato ba tsammani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.