Gwamna Yari ya yi barazanan kashe sanata Marafa a siyasance a 2019
Sakamakon cewa gwamnan jihar Zamfara da mataimakinsa ne masu alhaki a kashe-kashen da ke faruwa a jihar Zamfara, gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, ya lashi takobin kashe sanata mai wakiltan Zamfara ta tsakiya a siyasance idan zaben 2019 ya zo.
Gwamnan ya yi magana ne da yawun daya daga cikin masu bashi shawara, Alhaji Salisu Isah, a wani hira da manema labarai a Kaduna inda yace, “sanatan ya bayyana halin zambanshi kuma ya zama wajibi in mayar masa da martani akan zarge-zargen da yayi saboda mutane su san waye Sanata Kabiru Marafa.
“Wajibi ne a sanar da jama’a cewa gwamna Yari ya zange dantse wajen dakile rashin tsaron da ke barazana ga mutanen jihar Zamfara kuma kamata yayi a yabesa ba kushesa ba.”
Yayinda yake amsa tambayar yan jarida a kan maganar Sanata Marafa cewa duk abinda ya faru da shi a kama gwamna Yari, Alhaji Sa’idu yace: “A hakane, zamu kasheshi a siyasance kuma zamu birne siyasarshi a 2019. So yake ya zama gwamna a 2019, ba zai samu ba, ko majalisar ba zai koma ba."
KU KARANTA: Masu kudi sun fara barin jihar Legas saboda yawan haraji da suke biya - Rahoto
“Sanata Marafa nuna cewa shi magoyi bayan shugaba Buhari ne amma a gaske, makiyinsa ne. Ina kira ga shugaba Buhari da shugaban majalisar dattawa yayi hankali da munafukai irin Sanata Marafa.”
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng