Manyan Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Na Karfi Tsakanin Sojojin Najeriya Da Na Nijar

Manyan Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Na Karfi Tsakanin Sojojin Najeriya Da Na Nijar

Najeriya da Jamhuriyar Nijar na iya gwada kwanji nan da makonni biyu idan ba a cimma yarjejeniyar zaman lafiya a kan lokaci ba.

A ranar Laraba, 26 ga watan Yuli, Janar Abdourahamane Tchiani ya hambarar da gwamnatin Mohammed Bazoum a wani juyin mulkin da ba a zubar da jinni ba da ya sha suka a kasashen duniya da dama.

A daya bangaren kuma kungiyar ECOWAS ta yi yunkurin ganin an cimma matsaya na zaman lafiya da shugabannin mulkin soja a Nijar amma hakan bai cimma ruwa ba.

Karfin sojin Najeriya da na Nijar
Najeriya da Nijar: ECOWAS a tsakani | Hoto: @OfficialABAT/Twiter, Christopher Pillitz, and Télé Sahel/AFP
Asali: Getty Images

Tuni dai shugaban kungiyar ECOWAS kuma Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya tuntubi majalisar dattawa domin amincewa da amfani da karfin soja a Nijar.

A wannan takaitaccen rahoton, mun yi nazari kan muhimman abubuwa guda biyar da ya kamata ku sani idan Nijar da Najeriya za su shiga fada a fagen daga.

Kara karanta wannan

Mun fi karfinku: Jigon APC ya gargadi sojojin Mali, Nijar da suke barazanar taran na Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Matsayin Soja

Bisa kididdigar da Global Firepower ta yi a 2023, sojojin Najeriya na a kan matsayi na 36 a duniya, yayin da sojojin Najeriya ke a matsayi na 119.

Najeriya ce ta hudu a matsayin soja a naahiyar Afirka, yayin da Nijar ke kan matsayi na 25.

2. Yawan Sojoji

Jimillar sojojin Najeriya 215,000 ne, kuma wadanda ke kan aiki sun kai 135,000.

Najeriya na da sama da sojoji 85,000 da suke shirye da aiki da sauran jami’an tsaro 80,000.

A halin da ake ciki, Jamhuriyar Nijar za ta iya alfahari ne da sojoji 13,000 kacal, wanda bai kai 15% cikin 100% na sojojin Najeriya ba.

Nijar na da jami’an da ke bakin aiki 10,000 ne kacal kuma babu ko daya a matsayin sojin ko ta kwana.

3. Kasafin Kudi a Fannin Tsaro

Kara karanta wannan

Ahir dinka: PDP ta ja kunnen Tinubu, ta ce kada ma ya fara yakar Nijar, ga dalili

Dangane da batun kudi kuwa, Najeriya ba sa’ar Nijar bace ba saboda kasafin tsaron Najeriya ya zarce na makociyarta Nijar nesa ba kusa ba.

Najeriya dai na da kasafin kudin tsaro na sama da dala biliyan 3, yayin da makwabciyarta Nijar ke da kasafin kudin tsaro na dala miliyan 287 kacal.

Adadin siyayyar kayan aiki na Najeriya ya haura dala tiriliyan 1, yayin da na Nijar ya kai dala biliyan 28 kacal.

4. Makamai

A 2023, Najeriya na da tankokin yaki 177, yayin da Nijar ke da sifiri. Najeriya na da motocin sulke 15,748, yayin da Nijar ke da 728 kacal.

Makaman Najeriya masu sarrafa kansu sun kai 30 a yanzu, yayin da Nijar ba ta da ko daya.

Hakazalika makaman atilare na Najeriya sun kai 338, yayin da Nijar ba ta da ko daya. Makaman roka na Najeriya sun kai 37, yayin da Nijar kuwa ba ta da ko daya.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Najeriya za ta shaida zanga-zangar likitoci da ba a taba gani ba, an fadi yaushe

5. Sojin Sama

Najeriya na da jiragen yaki 144, da suka kunshi jiragen yaki 14, jiragen horo 28, jirage masu saukar ungulu 52, jiragen yaki na musamman guda shida da dai sauransu.

A bangaren jamhuriyar Nijar kuwa, suna da jiragen yaki 16 ne kacal.

Sanatocin Najeriya sun yi maganar karshe kan batun tura sojojin Najeriya su yaki na Nijar

A wani labarin, Sanatocin Najeriya sun yi watsi da bukatar da Shugaba Bola Tinubu na neman izinin tura sojojin Najeriya zuwa jamhuriyar Nijar a matsayin wani bangare na muradin ECOWAS na maido da zababben Shugaban kasar Mohamed Bazoum.

An hambarar da Shugaba Bazoum ne a ranar 26 ga watan Yuli a wani juyin mulki karkashin jagorancin masu gadin fadar shugaban kasar, Vanguard ta tattaro.

Shugabannin ECOWAS a wani taro da suka yi a Abuja kwanaki hudu bayan haka sun ba wadanda suka yi juyin mulkin wa’adin kwanaki bakwai su maido da Bazoum kan kujerarsa.

Kara karanta wannan

Shikenan: Sanatocin Najeriya sun yi maganar karshe kan batun tura sojojin Najeriya su yaki na Nijar

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.