Kungiyar CAN Reshen Legas Ta Goyi Bayan Tinubu Kan Cire Tallafin Mai

Kungiyar CAN Reshen Legas Ta Goyi Bayan Tinubu Kan Cire Tallafin Mai

  • Kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN, reshen jihar Legas ta nuna goyon bayanta kan cire tallafi da Tinubu ya yi a kasar
  • Shugaban kungiyar a jihar, Stephen Adegbite shi ya bayyana haka a Abuja a jiya Alhamis 3 ga watan Agusta
  • Ya ce tabbas cire tallafi zai saka mutane cikin wahala amma ‘yan Najeriya za su fi kowa morar hakan

Jihar Legas – Kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN, reshen jihar Legas ta goyi bayan cire tallafi da Shugaba Tinubu ya yi.

Shugaban kungiyar a jihar, Stephen Adegbite shi ya bayyana haka a jiya Alhamis 3 ga watan Agusta a Abuja inda ya ce ‘yan Najeriya za su fi morar hakan fiye da gwamnati, Legit ta tattaro.

Kungiyar CAN ta goyi bayan cire tallafi, ta koka kan yajin aikin NLC
Kungiyar CAN Reshen Jihar Legas Sun Nuna Goyon Bayansu Kan Cire Tallafi, Sun Roki NLC Kan Yajin Aiki. Hoto: Dele Alake.
Asali: Facebook

Adegbite ya tunatar da NLC batun gyaran matatun mai

Kara karanta wannan

Abin da Shugaba Tinubu Ya Fada Mana a Aso Villa Inji Shugabannin ‘Yan Kwadago

Kungiyar NLC a ranar Laraba 2 ga watan Agusta ta yi zanga-zangar gama gari kan wasu matakai da Shugaba Tinubu ke dauka da ke kuntatawa talakawa da suka hada da cire tallafin mai.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Adegbite ya tunatar da kungiyar kwadago ta NLC da su sani akwai yarjejeniyar gyaran matatun mai a kasar don haka akwai tsari mai kyau na bunkasa tace man a kasar, cewar Daily Trust.

Ya ce 'yan Najeriya za su fi kowa morar cire tallafin

Adegbite ya ce:

“Yana kyau yadda kungiyar NLC ta janye zanga-zangar da ta ke yi, sako na gare su shi ne abin da ya kamata su na fada a kai shi ne yadda za a yi amfani da kudaden cire tallafi.
“Tabbasa cire tallafi zai kuntatawa mutane, a gaskiya duk wata gyara sai an sha wahala, irin wannan na bukatar lokaci kafin a ci nasara.”

Kara karanta wannan

Tantance Ministoci: ‘Yar Katsina ta Sharba Kuka Gaban Sanatoci da Tuna Mahaifinta

Faston ya ce a matsayinsa na Kirista ya na da damar yin magana kuma ya yarda da gwamnatin Tinubu ganin yadda ta nada mutanen da za su kawo sauyi a kasar.

Kungiyar NLC Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Idan FG Ba Ta Janye Kara Ba

A wani labarin, Kungiyar Kwadago ta Najeriya, NLC ta yi gargadi ga Gwamnatin Tarayya kan ci gaba da yajin aiki.

Kungiyar ta ce idan gwamnatin ba ta janye karar da ta shigar da kungiyar ba za ta shiga yajin aiki a ranar 14 ga watan Agusta.

Shugaban kungiyar, Joe Ajaero shi ya bayyana haka yayin ganawar masu ruwa da tsaki na kungiyar a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.