An Kona Gidan Mai Shari'a Haruna Tsammani Bisa Hukuncinsa Kan Tinubu? Gaskiya Ta Fito Fili

An Kona Gidan Mai Shari'a Haruna Tsammani Bisa Hukuncinsa Kan Tinubu? Gaskiya Ta Fito Fili

  • Jita-jita ta yaɗu sosai a yanar gizo cewa an ƙona gidan mai shari'a Haruna Tsammani na kotun zaɓen shugaban ƙasa
  • Mai shari'a Tsammani shi ne shugaban kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa, ƙarar da ƴan Najeriya ke bibiya sosai
  • Wasu rubuce-rubuce a soshiyal midiya a cikin ƴan kwanakin nan, sun yi iƙirarin cewa an farmaki gidan Tsammani, amma ba gaskiya ba ne kwata-kwata

FCT, Abuja - Wani shafin watsa labarai, Igbo Times Magazine, ya wallafa a shafinsa na Facebook da Twitter cewa ƴan daba sun ƙona gidan mai shari'a Haruna Tsammani.

Mai shari'a Tsammani babban alƙali ne wanda ya ƙara shahara bayan ta bayyana cewa shi ne zai shugabanci kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa.

Gaskiya ta bayyana kan batun kona gidan Haruna Tsammani
Ba gaskiya ba ne batun kona gidan Haruna Tsammani Hoto: @Igbotimesnews
Asali: Twitter

Jita-jita cewa an farmaki gidan Tsammani saboda hukuncinsa kan Tinubu

Wallafar da aka yi a shafin na cewa:

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Farmaki a Jihar Arewa, Sun Yi Awon Gaba Da Mutane Masu Yawa

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Da dumi-dumi: An ƙona gidan wani alƙali bayan zargin yin hukuncin son rai akan Tinubu. Ƴan daba sun shirya ƙona gidan alƙali bayan hukuncinsa kan Tinubu."

Wannan wallafar dai, mutane da dama sun yi ta yaɗa ta a soshiyal midiya.

Labaran ƙarya sun yi yawa akan shari'ar zaɓen Bola Tinubu

A yayin da ƴan Najeriya ke ci gaba da dakon jiran hukuncin kotun kan ƙararrakin dake ƙalubalantar nasarar Tinubu, wasu masu yaɗa ƙarya da ƙarairayi na ci gaba da yaɗa labaran ƙarya.

Wani rahoto ya fito wanda yake cewa ɗaya daga cikin alƙalai biyar na kotun, mai shari'a Boloukuoromo Ugo ya yi murabus bayan jam'iyyar APC ta matsa masa lamba.

Rahoton da kotun ta fito fili ta yi watsi da shi.

Ƙafin rahoton Murabus ɗin Ugo, kotun ƙoli ta musanta zargin cewa alƙalin alƙalai na ƙasa, Olukayode Ariwoola, ya tattauna ta wayar tarho da Shugaba Tinubu kan shari'ar zaɓen shugaban ƙasa, Channels tv ta rahoto.

Kara karanta wannan

Juyin Mulkin Nijar Vs ECOWAS: An Aike Da Sabon Gargadi Zuwa Ga Shugaba Tinubu

Gaskiyar yadda abun yake

Na farko, binciken da Legit.ng ta yi ya nuna cewa hoton da aka yi amfani da shi domin nuna ƙona gidan, hoto ne na kotun Igbosere a jihar Legas wacce ƴan daba suka ƙona a lokacin zanga-zangar #ENDSARS a shekarar 2020.

Na biyu, mai shari'a Tsammani da kotun zaɓen basu bayyana hukuncin da suka yanke ba akan shari'ar Shugaba Tinubu.

Saboda haka wannan wallafar da aka yi, ƙarya ce tsagwaronta.

Mai Shari'a Ugo Bai Yi Murabus Ba

A wani labarin kuma, an bayyana gaskiya kan batun jita-jitar da ake yaɗawa cewa mai shari'a Ugo na kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ya yi murabus.

Jita-jitar dai ƙarya ce tsagwaronta domin alƙalin bai yi murabus ba daga matsayinsa na ɗaya daga cikin alƙalan kotun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng