Juyin Mulkin Nijar: Na Damu Dangane Da Lafiyar Bazoum, Buhari Ya Yi Bayani

Juyin Mulkin Nijar: Na Damu Dangane Da Lafiyar Bazoum, Buhari Ya Yi Bayani

  • Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna damuwarsa kan abinda ya faru a jamhuriyar Nijar
  • Buhari ya bayyana juyin mulkin da aka yi wa Shugaba Mohammed Bazoum a matsayin abin damuwa da ɗaga hankali
  • Ya ce da shi da iyalansa sun damu matuƙa kan halin da Shugaba Bazoum da iyalansa suke ciki

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana damuwarsa dangane da juyin mulkin da sojoji suka yi wa shugaban ƙasar Nijar Mohammed Bazoum.

Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne ranar Juma'a ta shafinsa na Twitter.

Buhari ya ce ya damu kan halin da shugaban Nijar yake ciki
Buhari ya ce ya damu kan halin da shugaban Nijar Mohammed Bazoum da iyalansa suke ciki. Hoto: Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

Buhari ya ce ya girgiza kan juyin mulkin da aka yi a Nijar

Buhari ya ce ya yi matuƙar girgiza da yadda abubuwa suka kasance a jamhuriyar Nijar kamar yadda jama'a da dama suka yi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Shiga Ganawar Sirri Da Matasan Jam'iyyar APC Kan Batun Ministoci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce dole ne hankula su tashi saboda rashin sanin makomar dimokuraɗiyya da ake mulkar ƙasar da ita da ma sauran ƙasashen da ke makwabtaka da ita.

Ya kuma ce da shi da iyalansa sun damu matuƙa dangane da halin da Shugaba Mohammed Bazoum da kuma iyalansa suke ciki tun bayan juyin mulkin da ya wakana a ƙasar.

ECOWAS na ƙoƙarin shawo kan lamarin

Buhari ya kuma bayyana cewa, abin jin daɗi ne yadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayinsa na shugaban ECOWAS ke ƙoƙarin shawo kan matsalar yadda ya kamata.

Buhari ya yi fatan samun nasara wajen daƙile yunƙurin juyin mulkin da har yanzu bai gama tabbatuwa ba.

Sannan kuma ya yi fatan cewa, Shugaba Mohammed Bazoum tare da iyalansa na nan cikin ƙoshin lafiya.

Jaridar The Punch ta yi wani rahoto da ke cewa Janar Abdourahmane Tchiani, wanda shi ne ya jagoranci kifar da gwamnatin ta Bazoum, ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaban ƙasar Nijar.

Kara karanta wannan

‘Ba Batun Neman Minista Ba Ne’, Jonathan Ya Bayyana Dalilin Kai Wa Tinubu Ziyara

Bazoum ya ce zai ci gaba da kare martabar dimokuraɗiyya

Legit.ng ta yi rahoto a baya kan alwashin da hamɓararren shugaban Nijar Mohammed Bazoum ya sha na cewar zai ƙare martabar dimokuraɗiyya.

Bazoum ya yi wannan jawabin ne dai a wani saƙo da ya wallafa ta kafar sada zumunta a ranar Alhamis, 27 ga watan Yuli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel