Gwamnan Jihar Jigawa Ya Nemi 'Yan Najeriya Da Su Kara Hakuri Da Mulkin Tinubu
- Gwamnan jihar Jigawa ya buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara haƙuri kan wahalhalun da su ke sha a ƙarƙashin mulkin Tinubu
- Malam Umar Namadi ya bayyana cewa nan gaba kaɗan ƴan Najeriya za su fara darawa a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Tinubu
- Gwamnan ya kuma buƙaci ƴan Najeriya da su marawa shugaban ƙasar baya domin ya cimma manufofin da yake da su
Jihar Jigawa - Gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi, ya tabbatarwa da ƴan Najeriya cewa wuyar da ake sha saboda tsare-tsaren Shugaba Tinubu, zai haifar da ɗa mai ido nan gaba.
Gwamna Namadi ya bayyana cewa Shugaba Tinubu yana nufin alkhairi ga ƴan Najeriya inda nan bada daɗewa ba za su fara darawa kan sabbin tsare-tsaren da yake yi a ƙasar nan, rahoton New Telegraph ya tabbatar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da yake magana a ranar Asabar da daddare lokacin da aka ƴan asalin Hadejia mazauna Kano suka karrama shi.
An karrama gwamnan ne a ƙarkashin jagorancin shugabannin ƙungiyar ƴan kasuwa, Dr Bature AbdulAziz, da babban ɗan kasuwa Salisu Sambajo.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ƴan Najeriya za su dara a ƙarƙashin mulkin Tinubu
Gwamnan ya haƙiƙance cewa Shugaba Tinubu yana da nufin alkhairi ga ƴan Najeriya domin haka yakamata a goya masa baya ya cimma manufofinsa ga ƴan Najeriya.
A kalamansa:
"Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana da nufin alkhairi ga ƴan Najeriya. Abin da kawai ake buƙata shi ne fahimta goyon bayan ƴan Najeriya, saboda nan ba da daɗewa ba za su fara cin gajiyar cire tallafin man fetur da sauran tsare-tsarensa da ake kuka akan su."
Umar Namadi ya yi nuni da cewa har yanzu gwamnatin APC rarrafe take yi, saboda haka dole ne ƴan Najeriya su fahimci manufofin da gwamnatin take son cimmawa, wanda hakan zai samu ne kawai idan an kai zuciya nesa.
Gwamnan Jigawa Ya Kai Ziyarar Bazata a Asibiti
A baya rahoto ya zo cewa gwamnan jihar Jigawa, Mallam Umar Namadi, ya kai ziyarar bazata a wasu asbitocin gwamnatin jihar.
Gwamnan a yayin ziyarar ta sa ya tarar da wasu jam'ian kiwon lafiya na siyar da magungunan da gwmanati ta kawo domin rabawa kyauta ga ƙananan yara.
Asali: Legit.ng