Facebook Ta Dauki Dumi Yayin da Malamin Jami’a Ya Yi Barazanar Ladabtar da Dalibi Kan Ra’ayin Siyasa
- Malamin jami’ar Yobe ya jawo cece-kuce bayan yiwa dalibi barazanar ladabtarwa idan suka hadu a jami’ar
- Bincike ya nuna cewa, dalibin ya zagi malamin ne a kafar sada zumunta ta Facebook, inda malamin ya yada hoton siyasa
- Ya zuwa yanzu, malamin ya yi bayanin gaskiyar abin da yake nufi da ladabtarwa da kuma daukar mataki
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Facebook - Wani malamin jami’a a Arewacin Najeriya ya jawo cece-kuce bayan da ya zargi wani dalibi da zaginsa a kafar sada zumunta ta Facebook.
Dr Sherrif Muhammad Ibrahim, wanda malami ne a jami’ar jiha ta Yobe, ya yada wani hoton gwmanan jihar, inda ya bayyana yabonsa ga kokari, jajircewa da kuma karbuwar da gwamna Buni ya yi a Yobe.
A kasan rubutun nasa ne wani dalibin jami’ar mai suna Hamisu Usman ya yi martani da kalaman da ba su dace ba, inda ya kiran malamin jami’ar da dan maula.
Za mu hadu a YSU, Dr. Sherrif
Wannan yasa, Dr. Sherrif ya tamka masa, inda ya ce tabbas za su hadu a jami’ar ta YSU kuma zai ladabtar da shi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Lamari dai ya dauki kamari, mutane da yawa na ta neman bahasi kan meye manufar malamin da kuma abin da zai yiwa dalibin.
Wasu na bayyana ra’ayin cewa, ai ba komai bane don dalibin ya yi masa rashin da’a tun da shi kansa bai kame kansa ba ya tallata ra’ayin siyasa.
A bangare guda, wasu na ganin rashin kirkin dalibin, inda suka nemi ya janye kalamansa tare da ba malamin hakuri.
Ga rubutun farko da Dr. Sherrif ya yada:
Dr. Sherrif ya yi bayani
A wani sabon rubutun da ya yada, Dr. ya yi bayani, inda yace mutane suna da saurin yanke hukunci kan batun da ba su fahimta ba.
Ya ikrarin cewa, ba lallai ya zama zai cutar da dalibin ba, watakila ma kyauta zai masa tare da yi masa nasiha kan abin da ya aikata.
Hakazalika, ya yi tsokaci da cewa, aikinsa na malanta ya daura masa yin tarbiya da kuma ladabtarwa a yanayi irin wannan.
Ga abin da yake cewa:
“Abunda na sani shine kowanne mutum idan ya yi rashin tarbiya ana gyara ma shi, kuma a sani na an fi tsammanin gyaran daga wajen iyaye ko malamai, kuma ni malami ne tsawon shekaru 19.
“Yau dalibi a jamiar da na ke karantarwa ya zage ni ya kira ni da sunan banza, sai na ce ma shi "Nagode amma zamu hadu a jami'ah" shikenan ban kara uffan ba, ban ce ga abunda zan ma shi ba, kawai cewa na yi zamu hadu, watakila ma nasiha zan ma shi koin bashi wata kyauta.
“A sani na babu dalibi nagari da ya fi karfin malamin shi ya ladabtar da shi, kuma duk wanda malami bai ladabtar da shi ba to tabbas baya samun cikakkiyar tarbiya.
“To yanzu ku da kuke ta cece-ku-ce me kuke nufi, shin taimakon yaron kuke yi kenan da barin shi ya zage malamin shi, ko kuma dai ba ku san me ake nufi da ladabi da biyayya ba ne?
“Ikon Allah.”
Malamin Jami'a a arewa ya rasa aikinsa saboda lalata da dalibansa mata
A wani labarin na daban, jami'ar jihar Kwara da ke Malete, ta sallami daya daga cikin malamanta, Pelumi Adewale, bisa zargin yunkurin lalata da dalibarsa, Tosin Adegunsoye.
Mataimakin shugaban KWASU, Mustapha Akanbi, shine ya bayyana haka a Ilorin ranar Litinin, yayin da yake fira da manema labarai kan bikin yaye dalibai karo na 8 da 9.
Akanbi yace tsohon malamin ya yi amfani da kasancewarsa daya daga cikin lakcarorin jami'ar KWASU wajen ɓata mata suna a idon mutane, kamar yadda Punch ta ruwsito.
Asali: Legit.ng