Rahotanni: Masu garkuwa da mutane sun fito da Malamin Jami’a, Dr I. G. Bako

Rahotanni: Masu garkuwa da mutane sun fito da Malamin Jami’a, Dr I. G. Bako

-Kwanakin baya masu garkuwa da mutane sun aukawa Jami’ar ABU Zaria

-A wani hari da aka kai a cikin tsakar dare ne aka sace Dr. Ibrahim G. Bako

-Iyalan wannan Malami sun tabbatar da cewa an fito da shi ranar Alhamis

Jaridar Sahelian Times ta fitar da rahoto cewa malamin jami’ar ABU Zaria da aka sace, Dr. Ibrahim G. Bako, ya samu ‘yanci har ya koma gida.

Ibrahim G. Bako wanda aka dauke har gida a ranar 23 ga watan Nuwamba ya shafe wata guda cur a hannun masu garkuwa da mutane kafin ya fito.

Idan za ku iya tunawa an bi wannan Bawan Allah ne har gidansa da ke unguwar BZ a cikin jami’ar ta Ahmadu Bello da ke Samaru, aka yi gaba da shi.

Darektan yada labarai na jami’ar ABU Zaria, Malam Auwalu Umar, ya shaida cewa an dauke wannan malami ne tare da mai dakinsa da ‘diyarsa.

KU KARANTA: An hallaka wani Malamin Jami'ar ABU Zaria

Daga baya an yi dace jami’an tsaro sun iya yin ta maza, sun bi wadannan miyagun ‘yan bindiga cikin daji, a haka aka ceto matarsa da kuma ‘diyarsu.

Rahotannin da mu ka samu a ranar Alhamis, 24 ga watan Disamba, 2020, sun tabbatar da cewa wannan malami ya dawo gida a lokacin sallar Isha’i.

Wani abokin aiki wanda yake makwabtaka da malamin a unguwarsu, ya tabbatar da wannan a shafinsa na sada zumunta da kimanin karfe 7:30 na dare.

Legit.ng Hausa ta samu labarin cewa ‘yanuwa da iyalan wannan mutum sun fito sun mika godiyarsu da daukacin jama’a da su ka dage da addu’o’i.

KU KARANTA: An bukaci N270m a hannun Daliban ABU da aka sace

Dr I. G. Bako Hoto: www.theabusites.com
Dr I. G. Bako Hoto: www.theabusites.com
Source: UGC

Kawo yanzu ba mu da labarin ko an biya kudin fansa kafin a fito da wannan malami da ke aiki a sashen koyar da kiwon lafiya a babbar jami’ar ta Arewa.

Ba wannan ne karon farko da jami’ar Ahmadu Bello ta gamu da matsalar garkuwa da mutane ba, a watan jiya an sace wasu dalibanta a kan hanyar Abuja.

Waɗanda aka yi garkuwa da su dalibai ne daga sashen koyon harshen Faransanci da ke hanyarsu ta zuwa wata gasa da aka shirya za ayi a garin Legas.

Kafin nan kuma masu garkuwa da mutane sun yi awon-gaba da wata malamar asibiti, wanda ta ke da alaka da wani babban Farfesa da ake ji da shi a jami’ar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel