Mutane 6 Sun Kwanta Dama Yayin da Wasu ’Yan Bindiga Suka Sace Manoma 40 a Kaduna

Mutane 6 Sun Kwanta Dama Yayin da Wasu ’Yan Bindiga Suka Sace Manoma 40 a Kaduna

  • Ana ci gaba da fuskantar tashin hankali a Arewa maso Yammacin Najeriya duk da kokarin jami’an tsaron yankin
  • An ruwaito yadda wasu ‘yan ta’adda suka hallaka malamin Izala da kuma wasu mutane a Birnin Gwari
  • Hakazalika, an ce sun yi awon gaba da wasu manoma sama da 40 a duk dai yankin na Birnin Gwari a Kaduna

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kaduna - Akalla mutane shida ne rahotanni suka ce wasu ‘yan bindiga sun hallaka tare da sace wasu 40 a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna, Channels Tv ta ruwaito.

Ko da yake har yanzu rundunar ‘yan sanda da gwamnatin jihar Kaduna ba su ce komai kan lamarin ba, shugaban kungiyar masarautar Birnin-Gwari (BEPU), Ishaq Usman Kasai, a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar ya ce an kai harin ne tsakanin Laraba da Alhamis din makon jiya.

Kara karanta wannan

Ganduje Ya Gamu da Cikas, Wasu Kusoshin APC Sun Faɗa Wa Tinubu Wanda Ya Cancanci Zama Shugaban APC Na Gaba

Kasai ya bayyana cewa dukkan mutanen shida manoma ne, ciki har da mataimakin shugaban kungiyar Jama’atul Izalatul Bid’ah Wa Iqamatus-Sunnah (JIBWIS), Malam Yakubu Muhammad Bugai.

Yadda aka hallaka mutane a Kaduna
'Yan ta'adda sun sace malamin Izala a Kaduna | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Sanarwar ta ce, an harbi malamin ne a ciki a gonarsa da ke kusa da yankin Rema, inda daga bisani aka dauke shi zuwa babban asibitin Jibril Mai-Gwari.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An sace manoma bayan kashe ‘yan uwansu

Ya kuma bayyana cewa, ‘yan bindigan sun kuma sace wasu manoma kusan 40 a wasu hare-hare daban-daban da suka kai.

Shugaban BEPU ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun yi awon gaba da jama’ar yankin a kusa da dajin Kuyambana wanda ya ce maboyar ‘yan tsagerun ne.

An kuma ce ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyen Unguwan Danfulani inda suka kashe mutum daya tare da yin garkuwa da wasu ‘yan uwa guda bakwai.

Kara karanta wannan

Assha: Wata Amarya Ta Datse Mazaƙutar Angonta Kan Abu 1 a Jihar Katsina

Daga bisani ‘yan ta’addan sun yi garkuwa da wasu ‘yan kasuwa guda shida a yammacin kasuwar mako-mako ta Birnin-Gwari.

'Yan bindiga sun kashe malami da wasu mutane hudu a Kaduna

A wani labarin, 'yan bindiga sun halaka wani malami da wasu mutane hudu a layin Lasan Tabanni da ke cikin karamar hukumar Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna.

Maharan sunyi garkuwa da mutane 16 a Dogon Dawa, Layin Mahuta da kauyen Tabanni da ke gabashin karamar hukumar, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

An samu wannan bayanin ne a wata takarda wacce jami’an tabbatar da tsaro da shugabanci na gari na Birnin Gwari suka saki, wacce shugabanta, Ibrahim Abubakar Nagwari ya sanya hannu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.