'Yan bindiga sun kashe mutane biyu, sun yi garkuwa da malami a Kaduna

'Yan bindiga sun kashe mutane biyu, sun yi garkuwa da malami a Kaduna

  • Mahara sun kai farmaki anguwar Kuregu da ke Wusasa a Zariya dake Jihar Kaduna
  • 'Yan bindigar sun kashe mutum biyu sannan sukayi awon gaba da wani malamin makarantar islamiyya
  • An tattaro cewa mummunan al'amarin ya afku ne a ranar Juma'a, 25 ga watan Satumba

'Yan bindiga sun kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da malamin tsangaya a yankin Kuregu da ke karamar Hukumar Zariya ta Jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne a ranar Juma'a, 24 ga watan Satumba, da misalin karfe 10 na dare lokacin da 'yan fashin suka kutsa cikin garin, jaridar Daily Post ta ruwaito.

'Yan bindiga sun kashe mutane biyu, sun yi garkuwa da malami a Kaduna
'Yan bindiga sun kashe mutane biyu, sun yi garkuwa da malami a Kaduna Hoto: The Nation
Asali: UGC

Wani mazaunin garin Kuregu, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Daily Trust cewa mutanen biyu da aka kashe ‘yan garin ne.

Ya ce wadanda abin ya rutsa da su sun kasance a inda bai dace ba a lokacin da bai dace ba saboda 'yan fashin sun zo ne suna neman gidajen masu hannu da shuni a cikin garin lokacin da suka ci karo da wadanda abin ya rutsa da su sannan suka harbe su kafin suka yi garkuwa da wani malamin tsangayan a cikin garin.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Hari Shinkafi Bayan Tura Wasiƙa, Sun Kutsa Ofisoshin 'Yan Sanda Sun Saci Bindigu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Aminiya ta kuma ruwaito cewa daya daga cikin almajiran malamin da aka sace mai suna Idris Abdulrazak, ya ce:

“Muna zaune gaban malam muna karatu sai ga wasu mutane dauke da bindigogi suna harbe-harbe suka shigo suka ce mu kwankwanta.
“Sai suka fito da malamimmu suka tasa shi gaba suka tafi da shi, sai kuma suka kama wasu yara biyu da ke kan babur din roba-roba suka hada su suka yi gaba da su.”

Kazalika, wani wanda ’yan bindigar suka je gidansa amma ya nemi a sakaya sunansa ya ce suna shirin kwanciya kenan sai kawai ya ji ana harbi da bindiga, inda ya kira ’yan banga tunda dama suna da lamboninsu sai suka ce basu ba ne.

A cewarsa wannan ne ya sa suka gane cewa ’yan bindiga ne, sannan ya kira ’yan sa kai a anguwar tare da jami’an tsaro.

Kara karanta wannan

An kama ma’aurata kan kashe dansu tare da binne shi cikin sirri saboda ‘rashin ji’

Sai dai ya ce ko kafin su zo har ’yan bindigar sun kashe yara biyu da suka dauko su a kofar gidansa.

An tattaro cewa jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Jalige ya yi alkawarin kiran waya bayan samun bayanai daga yankin amma bai yi hakan ba har zuwa lokacin kawo wannan rahoton.

'Yan sanda sun cafke wadanda suka yi garkuwa da daliban makarantar Bethel guda uku

A gefe guda, mun kawo a baya cewa yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane uku da ke da hannu a sace dalibai sama da 100 na makarantar Bethel Baptist, Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa jami’in hulda da jama’a na rundunar, Frank Mba ne ya gabatar da wadanda ake zargin, wadanda ke sanye da kayan sojoji, a hedikwatar runduna ta musamman da ke yaki da fashi da makami (SARS), a Abuja.

Kara karanta wannan

Gobara ta yi kaca-kaca da Hedkwatar hukumar NPA, dukiyoyi sun kone kurmus

Legit.ng ta tattaro cewa wadanda ake zargin, Adamu Bello, Isiaku Lawal da Muazu Abubakar, sun shaidawa manema labarai cewa su 25 ne suka sace daliban.

Asali: Legit.ng

Online view pixel