Yan Sanda Sun Kama Mutane 6 Bisa Zargin Fashi Da Makami a Bauchi
- Rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ta sanar da kama wasu mutane shida bisa zargin fashi da makami
- Rundunar ta ce tana kuma zargin mutanen da ta kama da ayyuka na daba ta hanyar amfani da muggan makamai
- Haka nan rundunar ta kuma kama wani matashi bisa laifin cirewa wani hannu ta hanyar amfani da wuka
Bauchi - Rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ta ce ta kama wasu mutane shida bisa zargin fashi da makami.
Rundunar ta ce ta kama mutanen ne ranar Lahadi, 23 ga watan Yuli a maboyarsu da ke rukunin gidaje na Nasarawan Madina da ke cikin garin Bauchi.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar, Ahmed Wakil ne ya bayyana haka a hedikwatar hukumar ranar Juma'a, kamar yadda jaridar The Punch ta wallafa.
Yadda Mutane Ke Amfani Da Lambar Mu Don Ciyo Bashi, Rundunar Yan Sanda Ta Bayyana Matakin Da Za Ta Dauka
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
'Yan fashin na da alaka da kunyiyoyin daba da sara suka
Wakil ya bayyana cewa jami'ansu sun yi nasarar kama mutanen shida ne a lokacin da suka fita wani rangadi na yammaci.
Ya ce bincikensu ya nuna musu cewa, mutanen da aka kama na da alaka da kungiyar 'yan sara suka da kuma dabanci da suka addabi al'ummar jihar.
Ya kuma kara da cewa binciken farko da suka gudanar, ya nuna musu cewa mutanen 'yan fashi ne kuma suna gudanar da harkoki na daba.
Haka nan ya bayyana cewa an samu makamai a hannunsu ciki kuwa har da wata sharbebiyar wuka da busasshiyar tabar wiwi.
Ya shaidawa manema labarai cewa, mutanen da ake zargi sun amsa laifukan da ake tuhumarsu da su baki ya.
An kama wani bisa zargin sarewa matashi hannu
Hankula Sun Tashi Yayin Da 'Yan Bindiga Suka Bindige Wasu Dalibai A Shagon Aski, 'Yan Sanda Sun Yi Martani
Kakakin rundunar 'yan sandan ya kuma bayyana cewa jami'ansu sun yi nasarar kama wani mai suna Muhammad Abdullah, saboda laifin sarewa wani matashi mai suna Mubarak Abdullahi hannu.
Ya ce jami'an nasu sun yi nasarar kamo Muhammad, wanda hukumar ta dade tana nema a maboyarsa da ke yankin sabon layi da ke Bauchi.
Ya ce wanda ake tuhuma ya aikata wannan danyen aikin ne wani lokaci a cikin shekarar 2021, tare da taimakon wasu abokansa guda biyu da har yanzu jami'an ke nema ruwa a jallo.
Ya kara da cewa rundunar ta baza komarta wajen ganin ta kamo sauran masu laifin don su zo su karbi hukunci daidai da abinda suka aikata.
An kama tsohon soja saboda safarar makamai ga 'yan ta'adda
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan wani tsohon soja da dakarun sojojin Najeriya suka cafke a jihar Bauchi saboda zargin safarar makamai ga 'yan ta'adda.
Binciken da sojojin suka gudanar, ya nuna cewa mutumin da ake zargi korarren soja ne daga cikin watan rundunar sojin da suka fafata yaki da 'yan Boko Haram.
Asali: Legit.ng