Sojoji Sun Cafke Tsohon Soja Mai Safarar Makamai Ga 'Yan Ta'addan Boka Haram a Bauchi

Sojoji Sun Cafke Tsohon Soja Mai Safarar Makamai Ga 'Yan Ta'addan Boka Haram a Bauchi

  • Dakarun sojoji sun cafke wani baragurbin tsohon soja wanda yake safarar makamai ga ƴan ta'addan Boko Haram
  • Dakarun sojojin cafke tsohon sojan ne a jihar Bauchi inda suka ƙwato makamai masu yawa a hannunsa
  • Ƴan ta'addan Boko Haram masu yawa sun ajiye makamansu tare da miƙa wuya ga dakarun sojoji a jihar Borno

FCT, Abuja - Hedkwatar hukumar tsaro ta ƙasa ta bayyana cewa an cafke wani tsohon soja mai safarar makamai da sauran kayan aiki ga ƴan ta'addan Boko Haram a ƙaramar hukumar Bogoro ta jihar Bauchi.

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da darektan watsa labarai na hukumar tsaron, Manjo Janar Edward Buba, ya fitar a ranar Juma'a 28 ga watan Yulin 2023, jaridar The Cable ta rahoto.

Sojoji sun cafke tsohon soja mai safarar makamai ga yan Boko Haram
Sojojin sun cafke tsohon sojan ne a jihar Bauchi Hoto: Thecable.com
Asali: UGC

Manjo Janar Edward Buba ya bayyana cewa an cafke tsohon sojan ne a ranar 18 ga watan Yuli, a garin Boi cikin ƙaramar hukumar Bogoro ta jihar Bauchi, rahoton Channels tv ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Ko Ganduje Zai Zama Shugaba? Jam'iyyar APC Ta Sanaya Ranakun Manyan Tarukanta 2

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A ranar 18 ga watan Yuli, dakarun sojoji sun cafke wani mai safarar bindigu a Boi cikin ƙaramar hukumar Bogoro ta jihar Bauchi."
"Binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin korarren soja ne daga rundunar sojoji ta 5 Bde a Damasak. Dakarun sojojin sun ƙwato ƙananan bindigogi guda biyu, da harsasai 8 masu ƙaurin 9 mm."

Sojoji sun halaka ƴan ta'adda da dama

Haka kuma darektan watsa labaran ya bayyana cewa dakarun sojoji sun halaka ƴan ta'adda da dama a sassa daban-daban na ƙasar nan a cikin watan Yuli.

Buba ya bayyana cewa sama da ƴan ta'adda 700 waɗanda suka haɗa da ƙananan yara suka miƙa wuya ga dakarun sojoji a jihar Borno.

Buba ya ƙara da cewa wani ƙasurgumin ɗan ta'addan Boko Haram mai suna Ali, ya miƙa wuya a hannun dakarun sojoji a Dogumba cikin ƙaramar hukumar Mafa ta jihar Borno.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Halaka Bayin Allah Masu Yawa a Wani Mummunan Hari a Arewacin Najeriya

Sojoji Sun Halaka Yan Ta'adda 59

A wani labarin kuma, dakarun sojoji sun halaka ƴan ta'adda 59 a fafatawar da suka yi da su a cikin faɗin ƙasar nan.

Dakarun sojojin sun kuma ƙwato muggan makamai a hannun ƴan ta'addan tare da ceto mutane masu yawa da suka yi garkuwa da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel