Hukumar NDLEA Ta Yi Nasarar Kama Buhuna 116 Na Tabar Wiwi a Kano

Hukumar NDLEA Ta Yi Nasarar Kama Buhuna 116 Na Tabar Wiwi a Kano

  • Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA), ta sanar da kama buhunan wiwi 116 a jihar Kano
  • Hukumar ta kuma bayyana cewa ta yi nasarar kama mutane biyu da ke da hannu a safarar wiwin da aka kama
  • Hukumar ta kuma ce ta shafe tsawon lokaci tana sa ido a kan kayan bayan bayanan da ta samu a kansu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kano - Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) reshen jihar Kano, ta sanar da kama buhunan wiwi 116 a jihar.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Sadiq Maigatari ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata kamar yadda The Punch ta wallafa.

NDLEA ta kama buhunan tabar wiwi 116 a Kano
Hukumar NDLEA ta ce ta kama buhuna 116 na tabar wiwi a Kano. Hoto: Leadership, NAN
Asali: UGC

Jami'an NDLEA sun dauki tsawon lokaci suna dakon kayan

Sadiq ya bayyana cewa sun kama wiwin ne a Garindau kusa da gadar Wudil a karamar hukumar Wudil ta jihar Kano.

Kara karanta wannan

FRSC Ta Yi Bayani Kan Hadarin Motar Da Ya Yi Sanadin Rasuwar Mutane 7 Da Jikkata 5 a Jigawa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce nauyin tabar wiwin da suka kama ya kai kilogiram 1,553.1 wacce take a buhuna daban-daban.

Sadiq ya alakanta nasarar da suka samu da sanya idanun da jami'ansu suka yi bayan samun bayanai masu muhimmanci dangane da safarar wiwi din.

A cewarsa, jami’an na su sun shafe watanni biyu suna bibiyar kayan, wadanda aka dauko su daga Lokoja zuwa Jigawa, kafin su samu nasarar kama su.

An kama mutane biyu da ke da alaka da tabar wiwin

Sadiq ya kara da cewa baya ga buhunan tabar ta wiwi da jami'an na NDLEA suka kama, haka nan ma sun yi nasarar kama mutane biyu da aka bayyana sunayensu da Jonathan Nuhu da kuma Muhammad Abubakar.

Nuhu dan kimanin shekaru 45 ya fito ne daga kauyen Kanke da ke jihar Filato, yayin da shi kuma Abubakar, dan kimanin shekaru 18 ya fito daga karamar hukumar Kumbotso da ke jihar ta Kano.

Kara karanta wannan

‘Yan Sandan Nasarawa Sun Bi Motar Da Aka Sace Daga Jihar Zuwa Taraba, Sun Kamo Mutane Biyu

Wani bangare na kalaman Sadiq Maigatari na cewa:

"Mun yi imanin cewa dukkan mutanen biyu da aka kama, suna cikin wata babbar kungiyar masu safarar tabar wiwi zuwa arewacin Najeriya da kuma rarraba su ga dillalai daban-daban."

Sadiq ya kuma ce biyu daga cikin masu jigilar wiwin sun yi nasarar tserewa a yayin da jami'an na NDLEA suka tarfasu, inda ya ce yanzu haka sun bazama nemansu kamar yadda The Guardian ta wallafa.

NDLEA ta kama dillalan kwaya sama da 600 a jihar Kano

Legit.ng a baya ta kawo muku wani rahoto kan dillalan miyagun kwayoyi 619 da NDLEA ta kama a fadin jihar Kano.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da aka bayyana cewa sama da mutane miliyan biyu ne ke ta'ammali da miyagun kwayoyi a fadin jihar ta Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel