Jami'an DSS Sun Sake Kama Emefiele Bayan Zaman Ƙotu a Legas

Jami'an DSS Sun Sake Kama Emefiele Bayan Zaman Ƙotu a Legas

  • Jami'an DSS sun sake damƙe tsohon gwamnan babban banki CBN, Godwin Emefiele bayan kammala zaman Kotu a Legas
  • Hakan ya biyo bayan taƙaddama da rikicin da ya auku tsakanin dakarun DSS da jami'an hukumar kula da gidajen gyaran hali
  • A ranar Talata, 25 ga watan Yuli, 2023, aka gurfanar da Mista Emefiele a gaban babbar kotun tarayya mai zama a Ikoyi

Lagos state - Jami'an hukumar farin kaya ta ƙasa (DSS) ta ƙara damƙe dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Mista Godwin Emefiele.

Jaridar Punch ta tattaro cewa jami'an DSS sun sake kama Emefiele kan suka yi awon gaba da hi daga harabar babbar Kotun tarayya mai zama a Ikoyi, jihar Legas.

Godwin Emefiele a Kotu.
Jami'an DSS Sun Sake Kama Emefiele Bayan Zaman Ƙotu a Legas Hoto: @MSIngawa
Asali: Twitter

Tun da fari, dakarun DSS da jami'an hukumar kula da gidsjen gyaran hali sun samu saɓani wanda ya kai ga rigima a tsakaninsu kan waɗanda ya dace su tafi da Emefiele.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Tsohon Shugaban APC da Sakatare a Villa, Bayanai Sun Fito

Yadda aka samu hayaniya a harabar Kotu kan Emefiele

Rundunar ‘yan sandan sirrin (DSS) ta kama Emefiele ne jim kadan bayan wata arangama da jami’an hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya NSC.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Emefiele, wanda ke tsare a hannun DSS tun watan Yuni, an gurfanar da shi a gaban kotu ranar Talata, 25 ga watan Yuli, 2023.

Mai shari’a Nicholas Oweibo ya bayar da belin gwamnan CBN wanda aka dakatar a kan Naira miliyan 20, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Alkalin kotun ya bayar da umarnin a tsare Emefiele a gidan yari har sai an cika sharuddan belinsa.

Sai dai maimakon a miƙa babban shugaban bankin ga jami’an gidan yari, hukumar DSS ta yi yunkurin dauke shi, lamarin da ya ci tura, har rigima ta kaure a tsakaninsu.

Kara karanta wannan

Emefiele: Bidiyon Rikici Tsakanin Jami'an DSS Da Na Gidan Yari Kan Tafiya Da Tsohon Gwamnan Babban Banki Ya Bayyana

Jami’an DSS da ke dauke da makamai sun fi jami’an gidan yarin yawa da ƙarfi, lamarin da ya kai ga cafke wani babban jami’in hukumar gidajen yari wanda ke aiki a gidan yarin Ikoyi.

Emefiele: Bidiyon Rikici Tsakanin Jami'an DSS Da Na Gidan Yari Kan Tafiya Da Tsohon Gwamnan Babban Banki Ya Bayyana

A wani rahoton na daban kuma Rikici ya ɓarke tsakanin jami’an DSS da jami’an NCS, waɗanda dukkansu ke ƙoƙarin ajiye shi a hannunsu.

Ma’aikatar shari’a ta tarayya ce ta gurfanar da Emefiele a gaban kuliya, bisa zargin mallakar makamai da alburusai ba bisa ka’ida ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel