Mutane 7 Sun Rasu Yayin Da Wasu 5 Suka Jikkata a Hadarin Mota a Jigawa

Mutane 7 Sun Rasu Yayin Da Wasu 5 Suka Jikkata a Hadarin Mota a Jigawa

  • Mummunan hadarin da ya faru a kan hanyar Birniwa zuwa Malammadorin jihar Jigawa ya lakume rayuka bakwai da jikkata mutane biyar
  • An bayyana cewa wadanda suka rasu a hadarin sun kunshi maza biyar da kuma mata guda biyu
  • Jami'in hulda da jama'a na hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), reshen jihar ne ya bayyana hakan a Dutse

Dutse, jihar Jigawa - Akalla mutane bakwai ne aka tabbatar da sun rasu, yayin da wasu biyar suka samu raunuka a wani hatsarin mota da ya afku ranar Litinin, a kauyen Kirila da ke kan hanyar Birniwa zuwa Malammadori na jihar Jigawa.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar kiyaye haddura ta tarayya (FRSC), Gambo Ibrahim ne ya tabbatar da hakan a wani rahoton hadurran ababen hawa da ya bayar a Dutse kamar yadda The Punch ta wallafa.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Fitaccen Ƙwararren Likita Yana Kan Aiki a Arewacin Najeriya

Mutane bakwai sun rasa rayukansu a Jigawa
Hadarin mota ya yi sanadin rasa rayukan mutane bakwai a Jigawa. Hoto: African Examiner
Asali: UGC

Maza biyar da mata biyu ne suka rasu a hadarin

Ya ce mutane biyar sun samu raunuka mabanbanta a hadarin da ya faru da misalin karfe 1:30 na rana a ranar Litinin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gambo ya ce wadanda suka mutun sun hada da maza biyar da kuma mata biyu, ya kuma kara da cewa an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Birniwa domin kula da lafiyarsu.

Duk da ya gaza tantance musabbabin hadarin, Gambo ya bukaci masu ababen hawa da su guji yin lodin da ya wuce ka'ida, da kuma karya dokokin tuki.

'Yan sanda sun kama likitan bogi a Jigawa

A wani rahoto da Legit.ng ta yi a baya, kun karanta cewa jami'an 'yan sandan jihar Jigawa sun cafke wani likitan bogi da ya dade yana durawa mutane gurbataccen magani.

Kara karanta wannan

‘Yan Sandan Nasarawa Sun Bi Motar Da Aka Sace Daga Jihar Zuwa Taraba, Sun Kamo Mutane Biyu

'Yan sandan sun bayyana cewa sun cafke mutumin mai suna Samuel David da ya dade yana sayar da magunguna ba bisa kai'ida ba da sunan cewa shi likita ne.

David ya yi ikirarin cewa shi likita ne da ke aiki a wani asibitin koyarwa da ke Dutse, babban birnin jihar Jigawa.

Gwamnan Jigawa ya kai ziyarar bazata a babban asibitin jihar

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan ziyarar bazata da gwamnan jihar, Malam Umar Namadi ya kai a babban asibitn Dutse.

A yayin ziyarar ta sa, gwamnan ya tarar da wasu malaman lafiya na sayar da magungunan da aka tanada don rabawa kyauta ga marasa lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel