Hukumar FIRS Ta Tara Tiriliyan 5.5 a Watanni 6, Harajin Da Ba a Taba Samu a Tarihi Ba

Hukumar FIRS Ta Tara Tiriliyan 5.5 a Watanni 6, Harajin Da Ba a Taba Samu a Tarihi Ba

  • Hukumar FIRS ta iya tara fiye da Naira Tiriliyan 5 daga farkon Junairu zuwa karshen watan Yuni
  • Muhammed Nami ya ce wannan ne mafi yawan kudin shigan da aka taba samu a tarihi a rabin shekara
  • Shugaban hukumar tara harajin ya gabatar da alkaluma da ya halarci taron NEC a fadar Aso Rock Villa

Abuja - Hukumar FIRS mai alhakin tara haraji a Najeriya, ta shaida cewa daga Junairu zuwa karshen watan Yunin 2023, ta samu Naira tiriliyan 5.5.

A tarihin Najeriya, Sun ta ce ba a taba yin lokacin da aka samu wadannan kudin shiga ba.

Shugaban FIRS na kasa, Muhammad Nami ya shaida haka a lokacin da yake gabatar da jawabi a kan kudin da ake sa ran samu daga haraji a 2023-2024.

Hukumar FIRS
Ofishin Hukumar FIRS Hoto: www.firs.gov.ng
Asali: UGC

An yi taron NEC a Abuja

Kara karanta wannan

Kowa Zai Samu: Gwamnati Ta Bayyana Yadda Rabon N8000 Na Tinubu Zai Wakana

Muhammad Nami ya yi magana a gaban majalisar tattalin arziki ta kasa watau NEC a taron da aka yi na ranar 20 ga watan Yulin 2023 a fadar Aso Rock.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jawabin shugaban hukumar yana kunshe da bayanin kudin shigan da ya shigo asusun Najeriya a bana, ya ce FIRS ta cin ma sama da 100% na burinta.

Rahoton ya ce abin da aka yi lissafin gwamnatin Najeriya za ta samu daga watan Junairu zuwa karshen Yuni N5.3tr ne, an iya zarce hakan da N200bn.

Harajin mai ya yi gardama

A cikin watanni shida na farkon shekarar nan, an tara Naira Tiriliyan 2.03 daga saida mai, wanda hakan bai kai Naira Tiriliyan 2.3 da aka ci burin samu ba.

Alhaji Nami ya ce harajin da su ka fito daga bangaren da ba na mai ba ya zarce Naira tiriliyan 2.98 da ake hari, sai da FIRS ta iya tatso Naira Tiriliyan 3.76.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Bukaci Majalisa ta nada Mutanen da Buhari Ya Ki Amincewa da su a Gwamnati

Rahoton The Cable ya nuna kudin da aka samu a watan Yuni ya fi na kowane yawa (N1.65tr).

Ana sa ran a tara fiye da N5.5tr yanzu

Mai taimakawa shugaban FIRS wajen sadarwa da yada labarai, Oluwatobi Wojuola ya ce ba a taba samun watan da gwamnati ta samu haraji kamar Yunin ba.

Hukumar ta na sa ran daga Yuli zuwa Disamba, a samu kudin shigan da ya wuce wanda ka samu a watanni shidan farko da su ka wuce na shekarar nan.

Dangote ya yi bajinta a Afrika

A wani rahoto da mu ka fitar, an ji yadda Alhaji Aliko Dangote ya zama na 124 a jerin Attajiran Duniya da dukiyar ‘Dan kasuwan Najeriyan ta karu da 5.8%.

Kamfanin simintin Dangote ya yi suna a Kamaru, Kongo, Sierra Leone da Sanagal da wasu kasashen Afrikan, a halin yanzu ana maganar ya mallaki $16.9bn.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng