Yadda Zulum Ya Mamayi Ma’aikatan Lafiya, Ya Ziyarci Asibiti Cikin Tsakar Dare
- Babagana Umara Zulum ya kai ziyara zuwa asibitin gwamnatin Gwoza a lokacin da mutane ke barci
- A nan Gwamnan Jihar Borno ya iske ana fama da rashin wuta, an bar masu jinya a mummunan hali
- Nan take Farfesa Zulum ya bada umarnin a gyara lantarki, ya yi alkawarin za a gyara asibitin
Borno - Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya nuna takaicinsa a game da rashin wutar lantarki da halin da ya samu asibiti.
Daily Trust ta kawo rahoto cewa Farfesa Babagana Umara Zulum ya ziyarci babban asibitin garin Gwoza, ya same shi a mummunan yanayi.
Mai girma Gwamnan ya je garin Gwoza a yankin kudancin Borno a ziyarar aikin kwana daya. Gwamnan ya bayyana haka a Facebook.
Ba yau Zulum ya fara wannan ba
Tun da ya shiga ofis a watan Mayun 2019, Gwamnan ya yi suna wajen irin wannan mamaya domin ganewa kan shi halin da abubuwa su ke ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A tsakar daren Lahadi, Farfesa Babagana Zulum da ‘yan tawagarsa su ka je asibitin gwamnatin, sannan kuma soki abubuwan da ya gani da idonsa.
"Bai kamata a samu muhimmin wurin kula da lafiya irin babban asibitin Gwoza ya rasa abubuwan more rayuwa irinsu lantarki ba.
Lamarin ya tozarta halin lafiyar da marasa lafiya su ke ciki kuma ya na kawo cikas ga irin kokarin kwararrun ma’aikatan lafiyarmu.
Ba mu zo nan domin zargin wani ba, mun zo ne domin neman mafita. Babu wanda ya sanar da ni mummunan halin da wurin nan yake ciki.
- Babagana Umara Zulum
Za a dauki matakin gyara
An rahoto Gwamnan yana cewa babu wanda za a wanke daga zargi kan halin da aka samu asibitin tun daga shi har shugaban karamar hukuma.
Gwamna Inuwa Yahaya Ya Rantsar Da Farfesa Njodi a Matsayin SSG, Ya Kaddamar Da Kwamitin Masu Ba Shi Shawara
Gwamna Zulum ya ce kowa ya gaza yin abin da ya kamata, amma ya sha alwashin za a inganta rayuwar marasa lafiya da kuma sauran al’umma.
Tun daga nan ya bada umarni a gyara wutar lantarki da sauran ayyukan da asibitin da yake nema, kuma ya raba kayan abinci ga mutanen garin.
Nadin Ministocin tarayya
Rahoto ya zo cewa hukumar DSS, EFCC da Majalisar Dattawa za su jawo mutanen Bola Tinubu su gagara zama Ministocin da za a nada kwanan nan.
Watakila tsofaffin Gwamnonin APC su na ruwa a sakamakon samun su da tafka rashin gaskiya, daga ciki har da wasu da su ka yi wa APC hidima.
Asali: Legit.ng