Kotu Ta Dage Sauraron Karar Da Ake Yi Wa Alhassan Doguwa Kan Zargin Kisan Kai

Kotu Ta Dage Sauraron Karar Da Ake Yi Wa Alhassan Doguwa Kan Zargin Kisan Kai

  • Babbar kotun tarayya mai zamanta a birnin tarayya Abuja ta ɗage sauraron ƙarar da ake tsakanin gwamnatin jihar Kano da Alhassan Ado Doguwa
  • Kotun ta ɗage sauraron ƙarar ne domin ba Antoni Janar na jihar damar yin duba kan rahoton ƴan sanda dangane da zargin kisan da ake yi wa Doguwa
  • Kotun za ta ci gaba da sauraron ƙarar a ranar 25 ga watan Satumba a tsakanin ɓangarorin guda biyu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Wata babbar kotun tarayya mai zamanta a birnin tarayya Abuja, ta ɗage sauraron ƙarar Alhassan Ado Doguwa, ɗan majalisa mai wakiltar Doguwa/Tudunwada da gwamnatin jihar Kano kan zargin kisan kai.

Kotun ta ɗage sauraron ƙarar ne domin ba gwamnatin jihar Kano dama ta yi nazari akan rahoton ƴan sanda kan zargin kisan da ake yi wa Alhassan Doguwa.

Kara karanta wannan

Biliyan N2.9: Babbar Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Tsohon Gwamnan Da Ake Zargi Da Karkatar da Kuɗaɗen Jiha

Kotu ta dage sauraron karar Ado Doguwa da gwamnatin jihar Kano
Kotu ta dage sauraron karar har zuwa watan Satumba Hoto: Abba_gida_gida/Hon Alhassan Doguwa TV
Asali: Facebook

Alƙalin kotun Donatus Okorowo, a ranar Juma'a, 14 ga watan Yuli ya ɗage sauraron ƙarar har zuwa ranar 25 ga watan Satumba, rahoton The Cable ya tabbatar.

Dalilin ɗage ƙarar da ake yi tsakanin Doguwa da gwamnatin jihar Kano

A zaman kotun na ranar Juma'a, Antoni Janar na jihar Kano, M. K. Umar, ya buƙaci kotun da ta ba shi lokaci ya yi duba kan rahoton ƴan sanda kan lamarin domin ya shirya martaninsa kan ƙalubalantar ƙarar da Doguwa yake yi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Umar ya bayyana cewa gwamnatin jihar ba tana neman Doguwa ba ne saboda rikicin da ya biyo bayan zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga watan Fabrairu , ko batun ɗaukar bindiga.

Ya ƙara da cewa ana neman Doguwa a jihar Kano ne saboda ya amsa tuhume-tuhumen da gwamnatin jihar ta ke masa kan zargin kisan kai.

Kara karanta wannan

Sunayen Gwamnonin APC, PDP Da A Halin Yanzu Ke Kokarin Kwaton Kansu A Kotu Kan Matsalar Takardun Karatu

Ko da alƙalin kotun ya tambayi Antoni Janar ɗin ya karanta rahoton ƴan sandan, Umar ya bayyana cewa bai samu ya duba abinda rahoton ƴan sandan ya ƙunsa ba.

Alƙalin ya bayyana cewa rahoton ƴan sanda shi ne na biyu na binciken ƴan sandan wanda ya nuna cewa Doguwa baya da hannu a kashe-kashen da aka yi a lokacin zaɓen, cewar rahoton Vanguard.

Lauyan gwamnatin jihar ya buƙaci a ɗage ƙarar domin ba shi dama ya yi duba kan rahoton domin sanin mataki na gaba da gwamnatin jihar za ta ɗauka.

Kotu Ta Hana Gwamnatin Kano Cafke Doguwa

A baya rahoto ya zo cewa wata babbar kotun tarayya ta dakatar da gwamnatin jihar daga yunƙurin cafke Alhassan Ado Doguwa, ɗan majalisa mai wakiltar Doguwa/Tudunda.

Gwamnatin jihar ta Kano tana neman cafke Ado Doguwa ne domin ya amsa tuhume-tuhumen da ta ke masa kan zargin aikata kisan kai a lokacin zaɓe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel