Kotu Ta Dakatar Da Gwamnatin Jihar Kano Daga Sake Cafke Doguwa Bisa Zargin Kisan Kai

Kotu Ta Dakatar Da Gwamnatin Jihar Kano Daga Sake Cafke Doguwa Bisa Zargin Kisan Kai

  • Wata babbar kotun tarayya mai zamanta a Abuja, ta dakatar da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf daga sake cafke Alhassan Doguwa kan zargin kisan kai
  • Mai shari'a Donatus Okorowo, wanda ya bayar da umarnin ya buƙaci duka ɓangarorin biyu da su tsaya akan hukuncin baya har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci
  • Doguwa, an cafke shi a ranar 28 ga watan Fabrairu a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano yana kan hanyarsa ta zuwa Abuja

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja- An dakatar da gwamnan jihar Kano da Antoni Janar na jihar daga sake cafke ko tsare ɗan majalisar wakilai, Alhassan Doguwa bisa zargin kisan kai.

Mai shari'a Donatus Okorowo na babbar kotun tarayya a Abuja shi ne ya sake bayar da umarnin a ranar Talata, 27 ga watan Yuni bayan lauyan wanda ɗan majalisar, Afam Osigwe ya shigar da ƙorafi, jaridar TheCable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Sokoto: An Yi Jana'izar Mahaucin da Jama'a Suka Kashe Bisa Zargin Ɓatanci Ga Annabi SAW, Shaidu Sun Bayyana Gaskiya

Kotu ta hana Abba Gida-Gida sake cafke Doguwa
An hana gwamnatin Kano sake cafke Ado Doguwa Hoto: Abba_gida_gida/Hon Alhassan Doguwa TV
Asali: Facebook

Ƴan sanda sun cafke Ado Doguwa a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano, yayin da yake kan hanyar zuwa birnin tarayya Abuja a ranar 28 ga watan Fabrairu.

Ana zargin Doguwa ne da jagorantar ƴan daba wajen halaka wasu mutum biyu yayin ƙona sakatariyar jam'iyyar NNPP a Kano. Zargin da ɗan majalisar ya musanta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Doguwa an gurfanar da shi a gaban wata kotun majistare a Kano inda daga bisani aka tsare shi a gidan kaso. Wata babbar kotu bayan ƴan kwanaki kaɗan ta bayar da belin doguwa akan N500m.

Sai dai an janye tuhumar da ake masa bayan masu shigar da ƙara sun bayyana cewa sun kasa samun hujjojin da za su danganta shi da laifukan da ake tuhumarsa da su.

Doguwa ya shigar da ƙara a ranar 20 ga watan Yuni domin hana gwamnatin jihar Kano sake cafke shi, cewar rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Magana Ta Fito: Shugaba Tinubu Ya Yi Ƙus-Kus da Buhari a Landan, Gaskiya Ta Bayyana

Alƙalin ya umarci ɓangarorin biyu da su tsaya har sai an kammala shari'a

A lokacin sake zaman kotun da aka yi a ranar Talata, Osigwe ya roƙi kotun da ta sake tsawaita umarnin da ta bayar a baya na ɓangarorin biyu sun tsaya akan hukuncin da ta yi.

Ya buƙaci kotun da ta sanya lauyan gwamnatin jihar, M.K Umar, wanda ya wakilci gwamnan jihar da Antoni Janar, da ya yo rubutun amincewa da hakan.

Umar, wanda tun da farko ya buƙaci kotun da ta kammala sauraron shari'ar ba tare da ɓata lokaci ba, ya tabbatarwa da alƙalin cewa gwamnatin jihar ba za ta ƙara ɗaukar wasu matakai ba har sai kotun ta kammala sauraron ƙarar.

Alƙalin kotun ya umarci ɓangarorin biyu da tsaya akan hukuncin baya, har zuwa lokacin da za a yanke hukunci akan shari'ar.

Ya ɗage cigaba da sauraron shari'ar har zuwa ranar 14 ga watan Yulin 2023.

Kara karanta wannan

NSA: Sabon Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaron Kasa Ya Kama Aiki Gadan-Gadan

'Yan Kasuwa a Kano Sun Yi Sallah Kan Rusau Din Da Aka Yi Musu

A wani labarin kuma ƴan kasuwar da rusau ɗin gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ritsa da su, sun gudanar da Sallar Nafila domin neman mafita a wajen Allah.

Ƴan kasuwan sun koka kan halin ƙuncin da gwamnatin jihar ta sanyasu a ciki inda suka ce ba a yi musu adalci ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel