“Duk Abun da Emefiele Ya Yi Da Amincewar Shugaban Kasa”: Lauya Na So a Kama Buhari

“Duk Abun da Emefiele Ya Yi Da Amincewar Shugaban Kasa”: Lauya Na So a Kama Buhari

  • Ana kira ga kama tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da hukunta shi sakamakon tsare dakataccen gwamnan CBN, Godwin Emefiele
  • Barista Kingdom Okere ne ya yi wannan kira a ranar Juma'a, 14 ga watan Yuli, yana mai cewa duk abun da Emefiele ya yi da ya ba da damar tsare shi dole sai da yardar Buhari
  • Ya bayyana cewa babu wani hukunci da gwamnan na CBN zai dauka ba tare da amincewar shugaban kasa kafin aiwatar da shi ba

An bukaci hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ta kama tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari kan lamarin dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.

Barista Kingdom Okere ne ya yi wannan kiran yayin wata hira a shirin kalaci na Arise TV a ranar Juma'a, 14 ga watan Yuli.

Lauya ya ce duk abun da Emefiele ya yi da yarda Buhari
“Duk Abun da Emefiele Ya Yi Da Amincewar Shugaban Kasa”: Lauya Na So a Kama Buhari Hoto: Nigerian Presidency/Anadolu Agency
Asali: Getty Images

Okere ya bayyana hakan yayin da yake martani ga sanarwar da DSS ta yi cewa sun gurfanar da Emefiele zuwa kotu.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Umarci Jami'an DSS Su Yi Gaggawar Sakin Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya

Sanarwar ta ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Jama'a na iya tuna cewa hukumar a 2022, ta bukaci kotu ta bata izinin tsare shi saboda wani binciken laifi."

Dalilin da yasa ya kamata a kama Buhari - Okere

A halin da ake ciki, Okere, ya ce ya zama dole DSS ta kama tsohon shugaban kasa Buhari sannan ta gurfanar da shi a kotu tare da Emefiele.

Ya ce hukuncin da Emefiele ya yanke yayin da yake matsayin gwamnan CBN ya samu yardar Buhari kuma cewa duk abun da Emefiele ya yi,, ubangidansa ya yi tare da shi.

Okere ya ce:

"Duk abun da Emefiele ya yi a matsayin gwamnan CBN yana da amincear shugaban kasa. Don haka, idan su (DSS) suna da abun da suke son tonowa dake da alaka da shi, ya kamata su sani cewa abun ma yana da alaka da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, kuma ya kamata su hukunta shi."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: DSS Ta Dauki Tsatsauran Matakin Kan Emefiele Yayin da Kotu Ta Zartar Da Hukunci

A sanarwar da ta fitar a ranar Alhamis, 13 ga watan Yuli, DSS bata bayyana kotun da ta kai Emefiele ba ko zarge-zargen da take yi masa.

Hukumar DSS ta gurfanar da Godwin Emefiele

A baya Legit.ng ta rahoto cewa hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gurfanar dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele a gaban kotu.

Peter Afunanya, kakakin hukumar DSS ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, 13 ga watan Yuli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel