Cire Tallafi: ’Yan Najeriya Sun Kushe Shirin Tinubu Na Raba N8000 Ga Gidaje 12m, Sun Fadi Mafita

Cire Tallafi: ’Yan Najeriya Sun Kushe Shirin Tinubu Na Raba N8000 Ga Gidaje 12m, Sun Fadi Mafita

  • Shugaba Bokla Tinubu ya sanar da cire tallafin mai a ranar 29 ga watan Mayu yayin bikin rantsarwa a Abuja
  • Tun bayan cire tallafin, ‘yan kasar ke koka wa ganin yadda komai ya sauya a kasar musamman harkar sufuri
  • Ganin irin halin da ‘yan kasar suka shiga, Tinubu ya ware N500bn don rabawa ‘yan Najeriya don rage radadi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja – Sugaban kasa Bola Tinubu ya bukaci karin bashin $800m daga Bankin Duniya wanda majalisar Dattawa ta amince masa.

A cikin kudin, Tinubu ya yi alkawarin ba wa gidaje miliyan 12 kudi har N8000 na tsawon watanni shida don rage radadin cire tallafi, cewar Legit.ng.

Cire Tallafi: ’Yan Najeriya Sun Kushe Shirin Tinubu Na Raba N8000 Ga Gidaje 12m
Shugaba Bola Tinubu Ya Ware N500bn Don Rabawa 'Yan Najeriya Saboda Radadin Cire Tallafi. Hoto: @DOlusegun.
Asali: Twitter

Tun bayan cire tallafin, ‘yan Najeriya da dama suka shiga cikin wahalhalu da tsadar mai da kuma hauhawan farashin kaya.

Kara karanta wannan

Hadimar Tinubu Ta Ayyana Bangaren da Gwamnatin APC Za Ta Maida Hankali a Kai

'Yan Najeriya sun kushe shirin Tinubu na ba da tallafin

‘Yan Najeriya da dama sun yi martini a kan wannan shiri na Bola Tinubu inda suke ganin hakan asarar kudi ne babu abin da zai rage.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani mai sharhi a kan harkokin siyasa, @IjeleSpeaks2 ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa duk wanda ya ba da wannan shawarar bai kamata a dauke shi da muhimmanci ba.

Ya ce kudin za su fi amfanan ‘ya’yan talakawa idan aka bude kamfanonin sarrafa kayan auduga da hada takalma da za su na tura kaya wa kasashen waje.

Ya ce:

“Duk wanda ya kawo wannan shawarar bai kamata a dauke shi da muhimmanci ba.
“Tun da kamfanonin sarrafa auduga suna aiki, meyasa ba za a sayi kekunan dinki ba a raba a jihohi 36 ko wane wata? A inganta masu hada takalma da kayan aiki, kai wadannan kaya kasashen Afirka ta Yamma kadai zai kawo kudi wa Najeriya.”

Kara karanta wannan

Ja Ya Faɗo-Ja Ya Ɗauka: ‘Yan Majalisar Tarayya Sun Amince a Kashe Masu N70bn

Martanin mutane a kan shirin raba N8000 wa gidaje 12m

Wasu mutane sun yi martane game da abin da ya rubuta a shafinsa na Twitter.

@jagabanolu:

“Ko waye ya kawo shawarar, shugaban kasa sai da ya karanta kafin amincewa.”

@masterIBM:

“Yafi kyau Gwamnatin Tarayya ta samar da bas bas masu amfani da bakin mai don rabawa a jihohi 36 da birnin Tarayya…yafi wannan shirmen.”

@jahbless016:

“Wannan dubu takwas din zai taimake su.”

@abdullahi:

“Wannan tsari bai kamata ba, ban ji dadin haka ba.”

Tinubu Ya Sanar Cewa 'Yan Najeriya 12m Za Su Samu N8,000 Na Watanni 6

A wani labarin, a kokarin rage radadin da 'yan Najeriya ke fama da shi, Shugaba Bola Tinubu ya sanar da ba da tallafi.

Tinubu ya ware N500bn don rabawa 'yan Najeriya domin rage musu radadin cire tallafin man fetur a kasar.

Shugaban ya sanar cewa za a raba wa gidaje miliyan 12 dubu takwas har na tsawon watanni shida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.