Kwararrun Likitoci Sun Yi Haramar Tafiya Yajin-Aikin Farko a Mulkin Bola Tinubu

Kwararrun Likitoci Sun Yi Haramar Tafiya Yajin-Aikin Farko a Mulkin Bola Tinubu

  • Nan da makonni biyu kungiyar NARD za ta tafi yajin-aiki idan gwamnati ba ta dauki mataki ba
  • Wannan zai iya zama na farko tun da Bola Ahmed Tinubu ya gaji Muhammadu Buhari a Mayu
  • Shugabannin NARD sun ce tun da aka yi zama makonni bakwai da su ka wuce, ba a waiwaye su ba

Abuja - A ranar Laraba, kungiyar NARD ta likitoci su ka tsawaita wa’adin da su ka ba gwamnatin tarayya domin a biya masu bukatu ko su yi yajin-aiki.

Premium Times ta ce likitocin kasar sun kara makonni biyu kamar yadda su ka sanar a karshen taron majalisar koli ta NEC da aka yi ta yanar gizo.

Jawabin bayan taron da aka fitar ya nuna an zargi gwamnatin tarayya da kin cika alkawuran da ta dauka bayan zaman 19 ga watan Mayu da aka yi.

Kara karanta wannan

Tsofaffin Janarori Sun Jero Shawarwarin Kawo Karshen Matsalolin Tsaro

Likitoci
Likitoci a asibitin Najeriya Hoto: Getty Images/Emmanuel Osodi
Asali: Getty Images

Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin biyawa likitoci bukatunsu, har su ka yi nasarar hana su tafiya yajin-aiki, sai dai har yau maganar ba ta kai ko ina ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shugaban NARD, Dr Orji Emeka Innocent, da Sakatare, Dr Chikezie Kelechi O da sakataren yada labarai, Dr. Umar Musa, su ka sa hannu a jawabin.

Shiru kamar an aiki bawa gida

Kungiyar NARD ta ce makonni bakwai da tsaida magana da gwamnati, amma har yanzu shiru su ke ji. Nan da 19 ga watan Yuli, za a shiga yajin-aiki.

Daily Trust ta ce idan dai ba dauki mataki ba, likitocin za su dakatar da zuwa aiki. Ba wannan ne karo na farko da su ka yi irin wannan barazana ba.

Fushinmu da Gwamnati - NARD

Da mu ka tuntubi Dr. Sulaiman Isa wanda shi ne shugaban kungiyar NARD na reshen asibitin ABUTH, ya fada mana dalilan da ya jawo za su tafi yajin-aikin.

Kara karanta wannan

Tinubu Zai Fuskanci Barazana, Lauyoyi 8 Za Su Kai Shi Kotu Kan Harajin Abin Hawa

Likitan ya ce tun zaman da aka yi a watan Mayu, har zuwa yanzu ba su sake jin labarin batunsu ba, ya zargi gwamnati da nuna masu halin ko-in-kula.

Dr. Isa ya ce ana fama da karancin likitoci a kasar nan kuma su na so ayi masu karin albashi baya ga kudin koyon aiki wanda duk ba a yi komai a kansu ba.

Shugaban kungiyar ya nuna akwai likitocin da har yau ba su samu alawus da ake biya na shiga hadari ba, kuma akwai jihohin da su ke bin bashin albashi.

Da Legit.ng Hausa ta nemi jin me zai hana NARD ta dakata sai an nada Ministoci, sai ya ce ko a watan Mayu, da manyan sakatarori aka zauna ba Ministoci ba.

Tinubu ya dauki haramar gyara tattali

A yau ne labari ya zo cewa Shugaban Najeriya ya sa hannu a sababbin dokokin tattalin arziki da nufin tausayawa talaka da ‘yan kasuwan kasar nan.

Dele Alake ya ce Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya soke harajin 5% a kan kamfanonin sadarwa, kuma Gwamnatin tarayya ta dakatar da yin karin haraji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel