Yaki Da Cin Hanci: Tinubu Zai Fi Buhari Lalacewa A Wannan Bangaren, Farfesan Kimiyyar Siyasa Ya Yi Hasashe

Yaki Da Cin Hanci: Tinubu Zai Fi Buhari Lalacewa A Wannan Bangaren, Farfesan Kimiyyar Siyasa Ya Yi Hasashe

  • Farfesan tsangayar siyasa, Babafemi Badejo ya soki salon mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari akan yaki da cin hanci
  • Farfesan ya ce duk da cewa Buhari bai tsinana komai ba, akwai alamun cewa Shugaba Tinubu zai fi shi lalacewa a yaki da cin hanci
  • Badejo ya bayyana haka ne yayin gabatar da lakca a jami’ar Chrisland da ke Abeokuta cikin jihar Ogun a yau Laraba 5 ga watan Yuli

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja – Wani Farfesan a tsangayar siyasa, Babafemi Badejo ya ce Shugaba Bola Tinubu sai yafi Buhari lalacewa kan yaki da cin hanci a kasar.

Farfesa Badejo ya ce duk da Buhari bai tabuka komai ba, akwai alamun Tinubu zai fi shi lalacewa musamman ta bangaren yaki da cin hanci.

Tinubu Na Iya Fin Buhari Lalacewa A Yaki Da Cin Hanci, Farfesan Kimiyyar Siyasa
Farfesa Babafemi Badejo Na Kimiyyar Siyasa. Hoto: Wikipedia.
Asali: UGC

Badejo ya bayyana haka ne yayin gabatar da lakca a jami’ar Chrisland da ke Abeokuta cikin jihar Ogun, Daily Trust ta tattaro.

Kara karanta wannan

A Maimakon Kujerar Minista, Shehu Sani Ya Fadi Abin da Ya Dace da Tsofaffin Gwamnoni

Farfesan ya ce Tinubu zai fi Buhari a bangarori da dama amma banda fannin cin hanci

Ya ce duba da yadda kumun ludayin Tinubu ya nuna, zai fi Buhari a wurare da dama, amma banda bangaren yaki da cin hanci, cewar rahotanni.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce:

“Fahimta ta ita ce tsohon shugaban kasa Buhari ya gaza tabuka komai a yaki da cin hanci, ya fara da kwaikwayon yaki da cin hanci na Majalisar Dinkin Duniya bayan ya kafa kwamiti wanda ba su tsinana komai ba.
“Bangaren Shugaba Tinubu, ya yi wuri a yanke masa hukunci, amma bisa dukkan alamu abin da ya yi a cikin wata daya, zai fi Buhari abin kirki amma ba ta bangaren yaki da cin hanci ba.

Ya ce Tinubu ba ya ko maganan cin hanci wanda hakan shi ne babbar matsalar

Kara karanta wannan

Dan Jaridan Najeriya Ya Lissafo Kura-kurai 6 Na Buhari Da Bai Kamata Tinubu Ya Yi Ba

Ya kara da cewa:

“Tinubu ba ya ma maganan cin hanci, abin da yake fada kawai shi ne alkalai za su ji dadi, kowa zai ji dadi, babu kasar da za su ji dadi ba tare da yaki da cin hanci ba, watakila ya sauya tunaninsa, ina masa fatan alkairi."

Dan Jarida Ya Lissafo Kura-kurai 6 Da Buhari Ya Yi, Ya Gargadi Tinubu Ya Guji Afkawa Tarkon

A wani labarin, wani dan jaridan Najeriya Mayowa Tijjani ya lissafo wasu kura-kurai da ya ce Buhari ya tafka a lokacin mulkinsa.

Mayowa ya ce wadannan kura-kurai na tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari abun gudu ne a wurin Tinubu.

Ya lissafo kura-kuran inda ya shawarci Shugaba Bola Tinubu da ya guji aikata su don ceto mulkinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel