Mamakon Ruwan Sama Ya Yi Awon Gaba Da Mutane 2 a Birnin Katsina
- Ruwan sama da aka shantaɓa a cikin birnin Katsina kamar da bakin ƙwarya, ya yi awon gaba da mutane biyu
- Ruwan ya mamaye sabuwar gadar kurɗe da kuma wasu sauran wurare da ke kusa da Ƙofar Kaura ta cikin birnin na Katsina
- Mazauna yankin sun bayyana cewa basu taɓa fuskantar matsalar ambaliyar ruwa da ta kai irin wannan ba
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Katsina - Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a birnin Katsina, ya mamaye gadar kurɗe ta Kofar Kaura wacce tsohon gwamnan jihar, Aminu Bello Masari ya gina a karshen shekarar 2022 da ta gabata.
Ambaliyar ruwan ta kuma yi awon gaba da mutane biyu a Sabuwar unguwa da ke cikin birnin na Katsina, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Mutane biyu aka tabbatar da mutuwarsu a ambaliyar ruwan
Wani mazaunin sabuwar unguwa ya bayyana cewa, abokinsa mai shekaru 19 na ɗaya daga cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su, tare da wani yaro ɗan kimanin shekara 8.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Hamza ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a Gadar Na Yalli, inda ya bayyana cewa iyayen abokin nasa sun yi ƙoƙarin ceto shi amma abin ya gagara.
Ya ce daga baya masu aikin ceto sun bazama neman gawar matashin da ruwan ya yi awon gaba da shi.
Ruwa ya mamaye ko ina a yankin da lamarin ya faru
Legit.ng ta tsinkayi wani bidiyo da mashahurin mai amfani da kafar sada zumunta ta fesbuk, mai amfani da sunan 'Wakeup Katsina-Youth', ya wallafa na kai tsaye kan yadda ruwan ya mamaye titin Na Yalli da ke cikin birnin Katsina.
A cikin bidiyon mai tsawon mintuna takwas da ya wallafa a fesbuk, ana iya ganin yadda ruwan ya mamaye duka titin, da kuma wasu gidaje da ke a gefensa.
Ya bayyana cewa basu taɓa fuskantar irin ambaliyar da aka yi musu ranar Talata ba a unguwar a duk ruwayen da ake yi a baya.
Ya bayyana cewa ruwan bai wuce mintoci 40 ba ana yinsa, amma ya mamaye ko'ina a wannan titin da ya wallafa bidiyon nasa.
Gwamnan Katsina ya bai wa alhazan jihar kyautar makudan kudade a kasa mai tsarki
Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ya bai wa alhazan jihar kyautar kudade N278m a kasa mai tsarki.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan, Malam Ibrahim Kaula ya rabawa manema labarai.
Asali: Legit.ng