Matar Aure Ta Roki Kotu Ya Raba Aurensu Da Mijinta Saboda Dawainiya, Ta Ce Shekaru 10 Ta Na Kula Da Shi
- Wata mata ta roki kotu ta taimakawa rayuwarta don raba aurensu da mijinta mai suna Solihu don samun hutu
- Matar mai suna Rofiat Ibrahim ta ce yau shekaru 10 kenan mijinta na kwance ba lafiya ita take nemo abinci da kuma maganin jinyarsa
- Ta ce ta gaji ganin yadda 'yan uwanshi suka barta haka ba tare da taimaka mata ba kuma 'ya'yansu hudu duk ita take kula da su
Jihar Kwara - Wata matar aure ta roki kotu da ta raba aurensu da mijinta saboda rashin lafiyarsa da ya shafe shekaru.
Matar mai suna Rofiat Ibrahim ya fadawa kotun da ke zamanta a Ilorin ta jihar Kwara cewar mijinta ya shafe shekaru 10 ya na jinya.
Ta ce mijin nata mai suna Solihu bayan kwanciyar shi babu wanda ya taba taimaka mata daga danginsa, ita take fama kullum, Vanguard ta tattaro.
“Na Nemi Uwar Mijina Ta Samo Mun Karamar Yarinya”: Matar Aure Ta Koka, Ta Saki Bidiyon Yarinyar Da Aka Kawo Mata
Matar ta ce ita take dawainiya kullum ga kuma kula yara
Ta ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ni kadai nake nemo abinda za a ci, 'yan uwan mijina sun bar dawainiyar a kaina ni kadai.
"Na bar mijina a shekarar 2019 tare da 'ya'yana guda hudu lokacin da dawainiya ya mini yawa."
Ta ce bayan ta gudu ta bar shi, sai 'yan uwansa suka kai shi hukumar jin kai, daga nan ya tsere ba a sake ganinshi ba.
Ta bayyana yadda mijin nata ya tsere bayan an kai shi inda za a masa jinya
Ta kara da cewa:
"Surakanai na sun dauke shi zuwa gidan jin kai bayan na gudu, amma ya tsere ba a sake ganinshi ba sai yau."
Alkalin kotun, Aminullah Abdul Lateef ya umarci a kula da Solihu domin samun damar mai da martani.
Alkalin kotun har ila yau, ya dage sauraran karar zuwa ranar 9 ga watan Agusta don jin martani daga bangaren Solihu.
"Ina Kaunar Mijina Duk da Yana Bugu Na Kamar Jaka" Wata Mata Ta Nemi Saki a Kotun Musulunci, Ta Gindaya Sharaɗi 1
Kotun Shari'ar Musulunci Ta Daure Lauyan Bogi Watanni 15 A Gidan Kaso A Kano
A wani labarin, wata kotun shari'ar Musulunci ta daure lauyan bogi watanni 15 a gidan kaso.
Kotun da ke zamanta a karamar hukumar Kiru ta jihar Kano na zargin Zaharaddin Sani Maidoki da cin amana da kuma damfara.
Kotun na kuma zargin Zaharaddin wanda dan asalin jihar Kaduna ne da bayyana kansa a matsayin dan jarida.
Asali: Legit.ng