Sulhu Da 'Yan Bindiga: Bukarti Ya Soki Shawarar Yerima, Ya Bayyana Matakin Da Ya Kamata Gwamnati Ta Dauka
- Masanin tsaro a Najeriya, Bulama Bukarti ya soki shawarar da tsohon gwamnan Zamfara ya bayar kan sulhu
- Bukarti ya ce wannan bai da ce a irin wannan lokaci ba, tunda an sha gwada hakan ba a ci nasara ba a baya
- Ya shawarci gwamnatin da ta yi maganinsu da karfin soja, a yayin haka za su iya tuba su kuma ajiye makamansu
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Shahararren masanin harkar tsaro, Bulama Bukarti ya soki tsohon gwamnan Zamfara, Ahmed Yerima kan shawarar da ya ba wa Shugaba Tinubu.
Sanata Yerima a ranar Litinin 3 ga watan Yuli yayin ganawarsu ya shawarci Shugaba Tinubu akan yin sulhu da 'yan bindiga.
Yerima ya tabbatar da cewa yin sulhun shi ne mafi alkairi akan nuna musu karfin soji.
Bukarti ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a ranar Litinin 3 ga watan Yuli.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Bukarti ya ce dole gwamnati ta yi amfani da karfin soji sabanin fahimtar Yerima
Ya ce dole gwamnatin Tarayya ta yi amfani da karfin soja don dakile harkar ta'addanci da 'yan fashin daji.
A cewarsa:
"Sulhu da 'yan bingiga na nufin zama da su a teburi daya don ba su wani abu da nufin neman wani abu.
"Yadda za a yi maganinsu shi ne amfani da karfi, Yerima ya na cewa a lallaba su idan sunki a yi amfani da karfin soja, an gwada haka a baya."
Ya ce a yayin amfani da karfn soji watakila su nemi ajiye makamansu
Ya kara da cewa:
"Abin da ya kamata a yi shi ne a nuna musu karfin soja, watakila su nemi tuba amma ba sulhu ba, don ba a sulhu da 'yan ta'adda da masu laifi."
Ya kara da cewa abin da ya kamata gwamnati ta yi shi ne ba wa wadanda suke son tuba da ajiye makansu dama, cewar rahotanni.
Ya rage wa gwamnati ta ga wani mataki za ta dauka na karbar tubansu ko kuma akasin haka.
Sulhu Da 'Yan Bindiga Ya Fi Kamata A Yi, Ahmad Sani Yerima Ga Tinubu
A wani labarin, Sanata Ahmed Yerima ya shawarci Shugaba Tinubu da ya yi sulhu da 'yan bindiga.
Tsohon gwamnan ya ce sulhu ne kadai zai taimaka wajen kawo karshen rashin tsaro a kasar.
Ya ba da misali irin yadda aka yi sulhu da 'yan ta'addan Neja Delta, ya ce irin shi ake bukata a Arewacin Najeriya.
Asali: Legit.ng