Cire Tallafi: Masu Biredi Sun Shirya Kara Farashi Saboda Tsadar Fulawa, Sun Ce Hakan Ya Zama Dole
- Kungiyar masu yin biredi a Najeriya (PBAN) sun shirya kara farashin biredi saboda cire tallafin mai a kasar
- Shugaban kungiyar, Emmanuel Onuorah shi ya bayyana haka yayin hira da 'yan jaridu inda ya ce ba su da zabi
- Ya ce kara farashin ya zama dole ganin yadda kayayyakin hada biredin duk shigo da su ake daga ketare
FCT, Abuja - Yayin da farashin kayan abinci ke kara hauhawa, masu siyar da biredi sun shirya kara farashinsu saboda yanayin tattalin arziki.
Masu biredin suka ce hakan ya zama dole ganin yadda aka cire tallafin mai a kasar da farashin Naira kasuwanni, Legit.ng ta tattaro.
Shugaban kungiyar masu yin biredi a Najeriya (PBAN) Injiniya Emmanuel Onuorah shi ya bayyana haka yayin ganawa da jaridar Vanguard.
Masu biredin suka ce hakan ya zama dole ganin yadda aka cire tallafi
Ya ce mafi yawan kayayyakin da ake hada biredin shigo da su ake yi Najeriya wanda hakan ya ke da alaka da farashin Naira a kasuwanni.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewarsa:
"Mafi yawan kayayyakin da muke amfani da su wurin yin biredin shigo da su ake Najeriya.
"Saboda haka dole farashin zai karu ganin yadda gwamnatin Tarayya ta mayar da Naira ta yi yawo a kasuwanni, yadda babban bankin kasar ba shi da iko akan farashin.
"Masu siyar da fulawa suna amfani da wannan dama na farashin Naira don kara kudin, hakan zai sa farashin biredi ya karu a bangaren mu.
"Karin farashin biredin kuma zai kawo cikas a cinikayya wanda hakan zai sa gidajen biredi da dama kullewa."
Ya ce matakin da Tinubu bai dace ba
Akan cire tallafi kuwa, Emmanuel ya ce hakan bai yi tsari ba ganin yadda gwamnatin ta cire ba tare da kawo wani tsari da zai tallafawa 'yan kasuwa ba.
Ya ce:
"Wannan mataki a ganinmu bai dace ba, ganin yadda babu wani tsari kafin cire tallafin da zai taimaki 'yan kasuwa da sauran 'yan kasa.
"Mafi yawan ma'akatan mu ba sa iya biyan kudin sufuri zuwa wurin aiki wanda hakan ke kawo cikas a harkar yin biredin."
Hauhawar farashin kaya ya karu da 15.63% a Najeriya
A wani labarin, hauhawan farashin kaya sai kara tashi ya ke a Najeriya musamman kayan masarufi.
Bincike ya tabbatar da cewa farashin kaya ya karu da kashi 15.63 a watan Disamba ta 2021.
Hukumar kididdiga ta NBS ce ta bayyana hakan a rahoton da ta fitar a ranar Litinin, 17 ga watan Janairu.
Asali: Legit.ng