Yadda Ake Tseren Samun Shiga Kwamitoci Masu Tsoka a Majalisar Dattawa da Wakilai

Yadda Ake Tseren Samun Shiga Kwamitoci Masu Tsoka a Majalisar Dattawa da Wakilai

  • Bayan kammala zabukan majalisar tarayya, abin da ya rage shi ne rabon mukamai da kwamitoci
  • Sanatoci da ‘yan majalisa su kan dage domin su samu shugabanci ko shiga cikin manyan kwamitoci
  • A yanzu kallo ya koma kan yadda za ayi wannan kaso yayin da majalisa ta dawo daga hutun sallah yau

Abuja - A halin yanzu, ‘yan siyasa su na kai-komo a majalisar tarayya domin ganin sun samu shugabanci ko akalla shiga cikin manyan kwamitoci.

The Nation ta ce an fara fafutukar samun kwamitoci da ake yi wa kallon masu tsoka a majalisa bayan Tajudeen Abbas da Benjamin Kalu sun lashe zabe.

A makon jiya Rt. Hon. Tajudeen Abbas ya kafa wani kwamiti da zai yi aikin rabon kwamitoci. Bisa al’ada, shugaban majalisa ke jagorantar kwamitin.

Majalisa
Shugaban Majalisar Wakilai, Hon Tajudeen Abbas, PhD Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

Kwamiti zai yi aikin rabo

Kara karanta wannan

Don ku nake yi: Abba Gida-Gida ya fadi gaskiyar dalilin rushe-rushen da yake a Kano

Wannan kwamiti na musamman yana da wakilci ‘dan majalisa daya daga kowace jiha. A yau Talata, 4 ga watan Yuli zai gabatar da sakamakon aikinsa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Rahoton ya ce sababbi da tsofaffin ‘yan majalisa duk sun dage wajen ganin an cusa sunansu a kwamitocin da ake ji da su kamar na sha'anin kasafin kudi.

Betara zai iya komawa kujerarsa

Ana zargin cewa an yi yarjejeniya da shugaban kwamitin kasafin kudi cewa zai koma kan kujerarsa, a kan haka ne ya janye takarar da ya yi niyya.

Haka zalika ana tunanin an yi wa Mukhtar Betara alkawarin cewa magoya bayansa za su samu mukaman shugabanni da mataimaka a wasu kwamitocin.

Kwamitocin da ake ji da su

Punch ta ce kwamitin kula da baitul-mali ne kurum dokar kasa ta san da zaman shi, kuma ana ware shugabancin kwamitin nan ne ga ‘dan jam’iyyar adawa.

Kara karanta wannan

Sanatoci 3 Su na Tseren Rike Mukami Mafi Tsoka Bayan Shugaba a Majalisar Dattawa

Sauran kwamitocin da ake kwallafa rai a kansu a majalisa sun hada da: kasafin kudin, tattalin arziki, da kuma harkar tsaro (sojojin sama, kasa da ruwa).

'Yan majalisa su kan maida hankali ga kwamitocin harkar kwastam da na tashohin ruwa.

Ba a bar Sanatoci a baya ba

A majalisar dattawa an kafa kwamitoci 69 a karkashin jagorancin Ahmad Lawan. Kwamitin kasafin kudi ya fi kowane kasuwa, sai kwamitin mai da gas.

Ana rade-radin Sanata Adeola Solomon ya na neman shugaban kwamitin kasafin kudi, sai watakila Jarighe Jarigbe ya samu rikon kwamitin harkar mai.

Bola Tinubu ya hadu da hafsoshin tsaro

Nuhu Ribadu da duka sauran sababbin hafsun tsaro sun yi zama Aso Villa, an rahoto NSA ya ce tsaro ya karu sosai a Najeriya a mulkin Bola Ahmed Tinubu.

A lokacin da su ka yi wa shugaban kasar godiya da ya ba su wadannan mukamai, shi kuma Bola Tinubu ya yi masu alwashi ya na tare da su dari-bisa-dari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel