Jini Na da Ya Hau Idan da a Ce Na Fadi Zaben Majalisar Dattawa, Inji Adams Oshiomhole

Jini Na da Ya Hau Idan da a Ce Na Fadi Zaben Majalisar Dattawa, Inji Adams Oshiomhole

  • Tsohon gwamnan Edo ya bayyana yanayin da yake ciki bayan lashe zaben sanata a zaben da ya gabata
  • Ya ce hawan jininsa zai hau idan da ace bai ci nasara a zaben da ya gabata ba, saboda wasu dalilai da ya fadi
  • Gwamnoni da yawa a Najeriya sun tsaya takarar sanata bayan kammala wa'adin mulkinsu, amma ba kowa ne ya yi nasara ba

Jihar Edo - Adams Oshiomhole, dan majalisar dattawa daga jihar Edo, ya ce da ace ya fadi zaben sanata, da jininsa ya hauhawa, Premium Times ta ruwaito.

Oshiomhole ya bayyana haka ne a yayin bikin da abokansa suka shirya masa bayan rantsar dashi a majalisar ta dattawa, wanda aka yi a gidansa da ke Iyamho, Etsako, Edo, ranar Asabar.

Mista Oshiomhole, wanda tsohon gwamnan jihar Edo ne ya fafata da wanda ya gaje shi a kujerar gwamna, Godwin Obaseki a zaben da aka gudanar a ranar 25 ga watan Faburairu.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Fitaccen malamin addini a Najeriya ya fadi a filin jirgin sama saboda tsananin rashin lafiya

Adams Oshiomhole ya fadi yanayin da zai shiga da ya fadi zabe
Adams Oshiomhole a daya daga cikin taruka | Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images
Asali: Getty Images

Jawabin da Oshiomhole ya yi

Da yake jawabi, ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Idan da baku zabe ni ba, ban sani ba, hawan jini na zai iya zuwa 240/360, wannan kenan, idan har ina raye.
“Saboda murnan da abokan hamayya ta za su yi zai kasance su zo su kulle karamar kofata su karya min 'yan kasusuwa, amma kuka ce a’a.”

Oshiomhole ya ce gwamnoni da dama sun yi rashin nasara a yunkurinsu na zama sanatoci a zaben bana, inda ya ce abin kunya ne a gare shi idan shi ma ya fadi, Daily Trust ta ruwaito.

Sakon Oshiomhole ga 'yan yankinsa a jihar Edo

Ya godewa al’ummar yankin Edo ta Arewa da suka zabe shi a matsayin sanata bayan da ya mulke su a matsayin gwamna a baya.

Ya kuma godewa jama’a da suka zabi shugaba Bola Tinubu a zaben shugaban kasa, inda ya kara da cewa gundumar Edo ta Arewa ce kadai gundumar da Tinubu ya samu nasara a fadin jihar Edo.

Kara karanta wannan

“Buhari Yana Landan Don Jinya Kamar Yadda Ya Saba”, Rafsanjani Ya Yi Zargi

Ya yi alkawarin yin aikinsa yadda ya kamata a matsayinsa na wakilin Edo ta Arewa, inda ya ba da tabbacin cewa, Tinubu zai yiwa jihar ta Edo ayyuka masu ma'ana.

Gwamnonin Enugu da Cross River sun fadi zaben sanata

A wani labarin, wasu gwamnonin Najeriya da suka tsaya takarar sanata a zaben bana sun sha kaye duk da kuwa kokarin da suka yi na neman nasara.

Daga cikin wadanda suka fadi, akwai Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu da kuma Gwamna Ben Ayade na jihar Cross River.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel