An Bada Sunayen Sojoji da Za Ayi wa Karin Matsayi Tun da Aka Yi wa Janarori 50 Ritaya

An Bada Sunayen Sojoji da Za Ayi wa Karin Matsayi Tun da Aka Yi wa Janarori 50 Ritaya

  • Za a samu jami’an sojojin sama, ruwa da na kasa da za ayi wa karin matsayi a dalilin ritaya da aka yi
  • Manyan sojojin Najeriya sun ajiye aikinsu bayan shugaban kasa ya nada wasu sababbin hafsoshin tsaro
  • Wajibi ne a cike duk gibin da za a bari na mukamai, saboda haka wasu sojojin za su samu karin girma

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Fiye da sojojin sama, ruwa da na kasa 50 za ayi wa karin matsayi a Najeriya a sakamakon ritaya da aka yi wa manyan jami’an tsaron kasar nan.

Sojojin da su ka kai matsayin Birgediya Janar da Kanal za su samu karin matsayi zuwa Manjo Janar da Birgediya Janar, Daily Trust ta kawo labarin.

Haka zalika za ayi wa sojojin ruwa da kuma sojojin sama irin wannan karin girma a Najeriya. Hakan ne zai bada damar a maye wadanda za su bar aiki.

Kara karanta wannan

Dakyar na sha: Da jini na ya hau idan na fadi zaben sanata, tsohon shugaban APC ya magantu

Sojojin Najeriya
Wasu Sojojin Najeriya Hoto: Defence Headquarters Nigeria
Asali: Facebook

Majalisar da ke kula da harkar karin matsayin jami’an sojoji ba tayi zama ba tukuna, amma rahoton ya nuna ‘yan aji na 43 a NDA za su samu karin girma.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A yanzu ana tattara sunayen jami’an sojojin da za a kai wa hukuma domin ayi masu karin girma.

Janarori sun yi ritaya da kan su

Wani bincike da aka yi ya nuna kusan duka ‘yan aji na 38 a makarantar NDA sun gabatar da takardun murabus a hedikwata tun a karshen makon jiya.

Wata majiya ta shaida cewa in ban da wasu ‘yan aji na 39 da aka yi wa sauyin wuraren aiki ba da dadewa ba, duk za su yi ban-kwana da gidan soja.

Hukumar da ke da hakkin tabbatar da karin girma a gidan sojojin ruwa, sama da kasa za su tantance sunayen da aka gabatar, kafin a kara masu matsayi.

Kara karanta wannan

Mutane 6 Sun Rasu a Borno Yayin Da Wani Bam Da 'Yan Boko Haram Suka Binne a Kan Hanya Ya Tashi

An fara nada mukamai

Wasu ‘yan ajin RC 40, 41 da 42 da sun kai matsayin Manjo Janar, Rear admirals da AVM sun samu mukamai a sanadiyyar sauye-sauyen da aka fara yi.

Manyan sojojin za su maye guraben da magabatansu su ka bari, kamar yadda aka saba.

Manjo Janar Taoreed Lagbaja ya rike wasu daga cikin ‘yan ajinsu a Hedikwatar sojojin kasa, ya fara ba su mukamai da nufin shawo kan matsalar tsaro.

Sojoji za su yi ritaya da kan su

Yau ne wa’adin da aka ba manyan Janarori su ajiye aiki a sakamakon canjin hafsoshi da aka yi. Legit.ng Hausa ta kawo maku rahoton a makon da ya wuce.

A madadin hafun tsaro na kasa, Manjo Janar Y. Yahaya ya sa hannu a takardar da aka fitar mai lamba DHQ/I5/PLANS/801/13 da ta fito daga Hedikwata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng