Shehu Sani Ya Yi Martani Mai Zafi Kan Tattaunawa Da ’Yan Bindiga, Ya Ce Bata Lokaci Ne Kawai
- sohon dan majalisa, Sanata Shehu Sani ya ce tattaunawar gwamnati da ‘yan bindiga bata lokaci ne
- Sani ya zayyano dalilai uku da yake ganin tattaunawa tsakanin gwamnati da ‘yan bindiga ba za ta yi tasiri ba a Najeriya
- Ya ce gwamnonin jihohin da suka yi kokarin tattaunawa da ‘yan bindiga a baya sun yi nadamar abin da suka aikata
Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana dalilai uku da yake ganin tattaunawa tsakanin gwamnatin tarayya da ‘yan bindiga ba za ta haifar da sakamako mai kyau ba a kasar nan.
Sani ya ce gwamnonin jihohin da suka yi kokarin tattaunawa da ‘yan bindiga a baya sun yi nadamar abin da suka aikata.
A cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, 2 ga watan Yuli, Sani ya ce ba addini, kabila ko jam’iyyar siyasa ce ta kafa tafiyar 'yan bindiga ba.
Dalilai 3 da yasa tattaunawa da ‘yan bindiga bata lokaci ne
Sani, wanda masanin siyasa ne ya lissafo jerin dalilansa kamar haka:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
- ‘Yan bindiga sun kafu ne don su tatsi na tatsa, su yi sace-sace da kashe-kashen mutanen da ba su ji ba ba su gani ba
- Na biyu, ’yan bindiga ba a karkashin wani shugabanci suke ba, gungun ‘yan ta’adda ne kawai
- Sun sha bamban da ISWAP da Boko Haram a ke kisa, garkuwa da mutane da kai hare-hare da sunan addini
Kalaman Shehu Sani kan tattaunawa da ‘yan bindiga
Sani ya rubuta cewa:
“Tattaunawa da ‘yan bindiga ba zai yi tasiri ba saboda wadannan dalilai guda uku; ba kungiya ce mai dauke da makamai da aka kafa domin neman wata manufa ta addini ko kabilanci ko siyasa ba, illa karbar kudi ta hanyar tatsa, sace-sacen mutane da kashe-kashen mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.
“Na biyu, ba su da gamayya a karkashin imuwar shugaba daya, kawai suna gudanar da barnarsu ne a matsayin gungun ‘yan ta’adda; na uku, abin da ya sa suke barna don kudi ne; suna kisa da sata ne don kudi.
“’Yan bindiga ba kamar ‘yan kungiyar Iswap da na Boko ba ne wadanda barnarsu na sace-sacen mutane, hare-haren ta’addanci da kashe-kashen jama’a ya alakanta da sunan addini ba.
"Tattaunawa da 'yan bindiga bata lokaci ne. Gwamnonin da suka gwada hakan daga baya sun yi nadama."
SSS ta janye kara kan mai tattaunawa da ’yan bindiga, Tuku Mamu
A wani labarin, hukumar tsaro ta farin kaya (SSS) a ranar Alhamis ta bayyana janye bukatar ci gaba da tsare Tukur Mamu, tsohon mai shiga tsakanin 'yan bindiga na sama kwanaki 60 bayan kama shi.
Idan baku manta ba, an kama Mamu ne a watan Satumba a kasar Masar bisa zargin hannu a ayyukan ta'addanci, Premium Times ta ruwaito.
Mamu na daya daga cikin wadanda ke tattaunawa da 'yan bindigan da suka sace fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.
Asali: Legit.ng