Kungiyar IPMAN Ta Yi Karin Haske a Kan Yiwuwar Litar Man Fetur Ya Koma N700
- Wani shugaba a IPMAN ya karyata labarin da yake yawo cewa farashin man fetur yana shirin tashi
- Dele Tajudeen ya ce hasashen da wani ya yi soki-burutsu ne kawai wanda ba zai zama gaskiya ba
- Kungiyar IPMAN ta ce tsadar da Dalar Amurka ta yi ba zai jawo farashin mai ya kai har N700 ba
Oyo - Kungiyar IPMAN ta ‘yan kasuwan mai sun yi watsi da jita-jitar da ke yawo a kan batun karin kudin litar man fetur daga kusan N500 a yau.
Vanguard ta ce kungiyar ta yi karin bayanin ne a ranar jama’a, ta na mai ba mutane shawarar su daina sayen fetur su boye saboda tsoron tashin farashi.
Shugaban IPMAN na reshen Kudu maso yamma, Alhaji Dele Tajudeen ya bayyana haka jiya a garin Ibadan da ke jihar Oyo, ya na musanya rade-radin.
Kowa ya kwantar da hankalin shi
"Ina so in ankarar da mutane su daina tada hankalinsu a kai, babu dalilin shiga cikin firgici, mu na kan batun, kuma babu wani abin da ke kama da haka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutane su kwantar da hankalinsu yanzu, su tabbata babu abin da zai jawo su rika sayen litar man fetur fiye da farashin da su ke sayen shi a halin yanzu.
Idan mu ka duba farashin da ke hannun NNPCL, sun fi manyan ‘yan kasuwa damar samun riba.
Saboda haka farashin saidawar su ne su ka sanar, ba su taba tsaida farashi ga ‘yan kasuwa ba."
-Dele Tajudeen
PM News ta ce Dele Tajudeen ya ce karanta labarai a jarida cewa wani ya na maganar fetur zai kara tsada, yake cewa hasashe ne wanda ba gaskiya ba.
‘Dan kasuwan ya tabbatarwa talaka cewa tashin Dalar Amurka zuwa N700 ko N800 ba zai jawo farashin fetur ya tashi a gidan mai daga N500 zuwa N700 ba.
Iyakar tsadar man fetur shi ne N550
Ina so in sanar da cewa ka da wanda ya saida man fetur a cikin Legas fiye da N515 zuwa N520.
A yau mafi tsadan mai a ko ina bai kamata ya wuce N550 ba; Lita a kan N510 a Legas, a jihar Ogun kuma zai zama tsakanin N500 da N520.
- Dele Tajudeen
Digiri ya yi tsada
Ana da labari ilmin boko yana neman zama sai wane da wane a Najeriya domin kudin karatun jami'a ya nunku kafin a murmure daga tsadar man fetur.
Dalibai za su rika kashe tsakanin N97, 000 zuwa N225, 000 duk shekara a wajen karatun digiri a jami'ar Bayero wanda ke karkashin gwamnatin tarayya.
Asali: Legit.ng