Mataimakin Shugaban Kungiyar Miyetti Allah Na Kasa Ya Bata Ba’a Gansa Ba

Mataimakin Shugaban Kungiyar Miyetti Allah Na Kasa Ya Bata Ba’a Gansa Ba

  • An nemi mataimakin shugaban kungiyar Miyetti Allah na kasa, Injiniya Munnir Atiku Lamido, an rasa ko sama ko kasa
  • Injiniya Lamido ya bar gidansa da ke jihar Katsina zuwa wani taro a jihar Kaduna a ranar Juma'a, 23 ga watan Yuni amma har yanzu ba a gansa ba
  • An tsinci motarsa da wayoyinsa a ciki a ranar Alhamis, 29 ga watan Yuni amma shi ba a san inda yake ba

Kungiyar makiyayan Najeriya ta Miyyeti Allah (MACBAN) ta sanar da cewar mataimakin shugabanta na kasa, Injiniya Munnir Atiku Lamido ya bata.

Kakakin kungiyar MACBAN na kasa, Alhaji Muhammad Nura Abdullahi, shi ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a, 30 ga watan Yuni, Daily Trust ta rahoto.

Kungiyar miyetti Allah
Mataimakin Shugaban Kungiyar Miyetti Allah Na Kasa Ya Bata Ba’a Gansa Ba Hoto: Peoples Gazatte
Asali: Twitter

Ya bar gidansa da ke Katsina da nufin zuwa Kaduna

Kara karanta wannan

Kano: NLC Za Ta Shiga Takun Saka Da Abba Gida Gida Kan Albashin Ma’aikata Fiye Da 10,000

Abdullahi ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Muna son sanar da jama'a da hukumomin tsaro cewa ba a ga Injiniya Munnir Atiku Lamido ba. Injiniya Munnir shine mataimakin shugaban MACBAN na kasa.
"Ya bar gidansa da ke jihar Katsina a ranar Juma'a, 23 ga watan Yunin 2023 da niyan tafiya zuwa Kaduna. Tun lokacin ba a gan shi ba."

Abdullahi ya ce an gano motar babban jigon kungiyar ta MACBAN a ranar Alhamis tsakanin Jos da Kaduna kusa da mararraban Jos da wayoyinsa a ciki.

"Duk wani kokari na gano inda yake ya ci tura zuwa yanzu."

Abdullahi bukaci duk wanda ke da bayanai masu amfani kan inda Lamido yake da ya tuntubi ofishin yan sanda mafi kusa ko su tuntubi ofishohin MACBAN a fadin kasar.

Majiya ta iyalinsa ta magantu

Wata majiya ta iyalin ta ce Lamido ya bar gidansa da ke Katsina a ranar Juma'a domin halartan wani taron mahukunta a Kaduna. Shi kadai ya tafi a motarsa.

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Jam'iyyar PDP Ta Yabi Tinubu Kan Matakan Da Ya Ke Dauka, Ta Ce Ya Yi Bajinta

Majiyar ta ce:

"Lokacin da ya isa Zaria (jihar Kaduna), ya kira sannan ya yi magana da iyalinsa. Ya ce yana so ya tsaya a wani gidan cin abinci ya ci. Daga nan iyalin sun gaza samunta a waya bayan sun gwada yin hakan sau da dama."

Duk wani kokari da dan uwansa, wanda shi ma shugaban MACBAN ne a jihar Katsina ya yi don samunsa ya ci tura domin dukka wayoyinsa biyu a kashe suke.

Rundunar yan sanda ta yi martani

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa kakakin rundunar yan sandan jihar Katsina, Abubakar Sadik, ya tabbatar da cewar Mista Lamido ya bata.

Shahararren likitan Bauchi, Farfesa Abdu Ibrahim Ya Kwanta Dama

A wani labari na daban, mun kawo a baya cewa Allah ya yi wa shahararren likitan kwakwalwa, Farfesa Abdu Ibrahim, rasuwa.

Farfesa Ibrahim ya rasu ne a asibitin koyarwa na jami'ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) da ke jihar Bauchi a arewa maso gabashin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng