Cire Tallafi: UN Ta Bayyana Irin Matsalolin Da Matakin Tinubu Ya Jawo A Arewacin Najeriya, Ta Fadi Alkaluma

Cire Tallafi: UN Ta Bayyana Irin Matsalolin Da Matakin Tinubu Ya Jawo A Arewacin Najeriya, Ta Fadi Alkaluma

  • Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana yadda aka samu karin yunwa a Najeriya musamman a Arewacin kasar
  • Wakilin majalisar a bangaren ba da tallafi, Matthias Schmale shi ya bayyana haka a ranar Laraba a Abuja
  • Ya ce akalla mutane 700,000 ne musamman kananan yara 'yan kasa da shekara biyar ke fama da yunwa a yankin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Majalisar Dinkin Duniya (UN) ta bayyana yadda yunwa ke kara yawa musamman a Arewacin Najeriya saboda cire tallafin mai da Shugaba Bola Tinubu ya yi.

Wakilin majalisar ta bangaren kawo dauki a Najeriya, Matthias Schmale shi ya bayyana haka a ranar Laraba 28 ga watan Yuni.

Tinubu ya cire tallafin mai wanda ya jawo matsaloli a Najeriya musamman Arewacin kasar
Shugaba Bola Tiunub Yayin Karbar Rantsuwa. Hoto: BusinessDay.
Asali: Facebook

Schmale ya ce akalla yara 700,000 ne 'yan kasa da shekara biyar ke fama da matsanancin yunwa a kasar, Legit.ng ta tattaro.

Kara karanta wannan

Sallah: Tsadar Raguna Ba Zai Hana Mu More Bikin Sallah Ba, 'Yan Najeriya Sun Magantu

Ya bayyana irin matsalolin da matakin Tinubu ya jawo a yankin

Ya ce wadannan yara na daga cikin mutane miliyan 4.3 da ke jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa da suke fuskantar matsananciyar yunwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

"Na taba zuwa jihar Borno da sauran jihohin guda biyu sau da dama, naga yadda iyaye mata ke fama da 'ya'yansu wadanda ke cikin 'ynwa a hukumomin tallafawa matsalar 'yunwa."

Schmale ya gargadi cewa wannan bala'i ya samu ne saboda tsawon shekaru da aka yi ana fama da rashin tsaro a yankin, wanda ya hana mutane da dama zuwa gona don samun abinci.

Ya kara da cewa matsalar da rashin tsaron ta kawo akwai sauya yanayi da ya jawo ambaliyar ruwa wanda ya shafi mutane fiye da miliyan hudu.

Arewa maso Gabas na kan gaba wurin fuskantar matsalar yunwa

Kara karanta wannan

Ba Ka da Tausayi: Peter Obi Ya Tsoma Baki a Rusau Din Kanawa, Ya Yi Wa Abba Gida Gida Kaca-Kaca

Rahotanni sun tabbatar da cewa a wani bincike da Majalisar Dinkin Duniya ta yi ya nuna cewa Arewa maso Gabas sun karbi kashi 25 daga cikin $1.3bn da aka bayar.

Sai dai matsalolin takin zamani da abinci da kuma babbar matsalar cire tallafin mai shi ya kara rikirkita al'amarin.

Cire Tallafi: Masu POS Sun Bayyana Sabbin Farashin Cire Kudi Da Turawa

A wani labarin, masu sana'ar POS sun bayyana sabon farashin cire kudi da turawa.

Kungiyar masu wannan sana'a ce reshen jihar Lagos ta bayyana haka ganin yadda aka cire tallafin man fetur.

Kungiyar ta ce farashin na iya yin kasa duba da wurin da mutum yake, amma saba doka ce yafi sabon farashin da aka saka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.