Matashi Dan Shekara 19 Na Shirin Yin Wuff Da Yarinya yar 17, Bidiyon Kafin Aurensu Ya Yadu

Matashi Dan Shekara 19 Na Shirin Yin Wuff Da Yarinya yar 17, Bidiyon Kafin Aurensu Ya Yadu

  • Wani matashi dan shekara 19 ya fada tarkon son yarinya yar shekaru 17, kuma suna shirin shiga daga ciki nan da yan watanni kadan
  • Masoyan sun garzaya dandalin TikTok don wallafa wani bidiyo domin sanar da cewar suna shirin aure kuma an samu mutane miliyan 1.1 da suka kalla
  • Jama'a sun yi martani kan bidiyon, amma mutane da dama sun taya masoyan murna sannan suka yi masu fatan samun zaman lafiya a gidansu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani matashi dan Najeriya wanda shekarunsa basu gaza 19 ba ya shirya auren kyakkyawar sahibarsa mai shekara 17.

Shafin @vhikkyedibles ne ya wallafa wani bidiyo da ke kunshe da labarin soyayya tsakanin matashin da yarinyar a dandalin TikTok.

Matashi da budurwarsa
Matashi Dan Shekara 19 Na Shirin Yin Wuff Da Yarinya yar 17, Bidiyon Kafin Aurensu Ya Yadu Hoto: TikTok/@vhikkyedibles.
Asali: TikTok

A bidiyon, matashin ya yi tsayuwar daukar hoto da kyakkyawar amaryar tasa, wacce ke cike da farin ciki kuma alamu sun nuna sun shirya ma auren sosai.

Kara karanta wannan

Sallah: Tsadar Raguna Ba Zai Hana Mu More Bikin Sallah Ba, 'Yan Najeriya Sun Magantu

Bidiyon matashin yaro da ke shirin auren yar shekara 17 ya yadu

Rubuce a jikin bidiyon, masoyan sun ce mutane na ta maganganu a kan shawarar da suka yanke na ci gaba da shirye-shiryen aurensu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Amma duk da abun da mutane ke fadi, a shirye suke su yi aure yayin da suka yi wa kansu lakabi da matasan ma'aurata.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@trustnobodyonearth ta ce:

"Na tuna lokacin da na yi aure ina da shekara 16 yanzu ga shi in aiki tukuru a matsayin uwa da uba domin biyan kudin makarantar yarana."

@Akiragrace ta ce:

"Allah zai kare wannan aure, ba za a samu uba kadai ko uba kadai ba a nan gaba a rayuwarsu da sunan Yesu. Allah zai zagayesu."

@Neth ta ce:

Kara karanta wannan

Yadda Matashi Ya Nemo Mafita Maimakon Siyan Man Fetur, Ya Mayar Da Janaretonsa Zuwa Mai Amfani Da Iskar Gas a Bidiyo

"Na auri dan shekara 24 ina da shekara 17. Yanzu shekarar aurenmu 16 da yara maza 4 a jere."

@Eina ta yi martani:

"Na yi aure ina da shekara 18 kuma ina makaranta lokacin, yanzu dana yana aji 2 kuma na kasance uwa mai alfahari."

@Ray ta yi martani:

"Ga ni nan a shekara 23 ina gwagwarmaya ina neman wanda zai soni ya kuma kula da ni."

Matashiya ta koka a intanet bayan tsohon saurayinta ya rabu da ita da juna biyu

A wani labari na daban, wata matashiyar budurwa ta koka bayan tsohon saurayinta da suka rabu ya barta da juna biyu.

Matashiyar wacce ta ce iyayenta sun bukaci ta bar masu gida saboda cikin jikinta, ta roki saurayin da ya zo ya kula da dansa da ke jikinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng