Iyaye Sun Mika 'Yarsu Ga ’Yan Sanda Bisa Zargin Jefar Da Jaririyarta, Ta Ce Tana Gudun Dawainiya
- Rundunar 'yan sanda a jihar Gombe sun karbi wata mata da iyayenta suka mika ta hukumar bisa zargin jefar da jaririyar da ta haifa
- Matar mai suna Aishatu Dauda ta haifi jaririyar ne watanni kadan da suka wuce inda ta ce ta nemi mahaifin yarinyar ba ta same shi ba
- Wata majiya ta tabbatar da cewa wani mai siyar da biredi ne ya tsinci jaririyar a bakin kotun majistare a ranar Juma'a 2 ga watan Yuni
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Gombe - Wata mata mai suna Aishatu Dauda mai shekaru 35 ta jefar da 'yarta da bata wuce watanni ba a kauyen Gudemunu da ke karamar hukumar Dukku cikin jihar Gombe.
Jinjirar da aka yasar din ba ta wuce 'yan watanni ba a duniya kamar yadda jaridar Daily Trust ta tattaro.
Iyayen sun mika ta ne ga 'yan sanda bisa rashin tabbas akan 'yar tasu
Iyayen matar sun mika ta ga jami'an 'yan sanda bayan da suka fahimci ba ta ma san halin da jaririyar take ciki ba tsawon wannan lokaci.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wata majiya ta tabbatar da cewa an tsinci yarinyar ne a bakin kotun majistare a ranar Juma'a 2 ga watan Yuni na wannan shekara.
A cewar majiyar:
"Ta fadawa jami'an 'yan sanda cewa wanda ya dirka mata cikin ya tsere ta neme shi ta rasa kuma ita ba za ta iya daukar dawainiyar jaririyar ba.
"Shiyasa ta dauki wannan mataki na jefar da ita don gudun daukar dawainiya tun da ba ta da hali."
An tsinci yarinyar ne a kusa da kotun majistare da ke kauyen
An tabbatar da cewa wani mai siyar da biredi ne ya tsinci jaririyar a ranar Juma'a 2 ga watan Yuni a kusa da wata kotun majistare.
Daga bisani mutumin ya kai rahoton ofishin 'yan sanda, yayinda suka dauki jaririyar ga wata mata don ci gaba da kula da ita, Punch ta tattaro.
Wannan matsala ba yanzu ne aka fara samu ba musamman a Najeriya, a kwanakin baya an tsinci wata jaririya kusa da wani kango a unguwar Mu'azu da ke birini Kaduna, kamar yadda rahotanni suka tattaro.
Mutane Sun Shiga Rudani Yayin Da Aka Tsinci Jariri Cikin Tsumma A Kaduna
A wani labarin, wani matashi ya tsinci wani jariri kwance cikin tsumma a unguwar Mu'azu da ke birnin Kaduna.
Matashin ya tsinci jaririn ne da safiyar Asabar 17 ga watan Yuni inda ya mika shi ga wani dan sa kai a yankin.
Dan sa kai din da ya bukaci a boye sunansa daga bisani ya mika jaririn ga ofishin 'yan sanda mafi kusa.
Asali: Legit.ng