“Har Yanzu Na Yarda Da So”: Matashiya Da Ta Taba Kokawa Bayan Saurayinta Ya Rabu Da Ita

“Har Yanzu Na Yarda Da So”: Matashiya Da Ta Taba Kokawa Bayan Saurayinta Ya Rabu Da Ita

  • Wata matashiya yar kasar Kenya wacce ta yi suna a 2019 saboda kuka da ta sharba a bidiyon TikTok bayan saurayinta ya rabu da ta, ta ba da labarin kanta
  • Nachi Lubanga ta bayyana cewa ta zuba jari na zuciya da kudinta a soyayyar, ciki harda biyan kudin hanyar gidansu kafin ya rabu da ita
  • Ta karfafawa sauran mutane gwiwar rungumar soyayya, samun farin ciki sannan kada su bari abubuwan da suka faru su hana su samun farin cikin da soyayya zata kawowa

Lubanga Nachi, wata matashiya wacce ta yi suna a 2019 saboda kuka da ta sharba a wani bidiyon TikTok bayan saurayinta ya rabu da ita, ta magantu a kan labarinta.

Matashiya tana sharbar kuka
“Har Yanzu Na Yarda Da So”: Matashiya Da Ta Taba Kokawa Bayan Saurayinta Ya Rabu Da Ita Hoto: Lubanga Nachi.
Asali: TikTok

Saurayi ya rabu da Lubanga Nachi bayan ta biya kudin haya

A wata hira da shahararriyar jaridar kasar Kenya, TUKO.co.ke, Nachi ta bayyana cewa ta zuba jari na zuciya da kudi a soyayyarta da Izoh, ciki harda biyan kudin hayar gidan da suke zaune.

Kara karanta wannan

"Bayan Wuya": Matashiya Wacce Ke Yawon Talla Ta Koma Turai, Ta Fara Aiki a Matsayin Malamar Asibiti

Sai dai kuma, Isoh ya kawo wata matar cikin gidansu sannan ya bukaci Nachi da ya barsu, yana mai ikirarin cewa ya samu sabuwar masoyiya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta ce:

"Na ji radadi sosai bayan ya zo gidanmu a Ruiru tare da wata macen sannan ya nemi na bar gidan. Ya fada mani cewa ya samu sabuwar masoyiya. Mun shafe shekaru biyar muna soyayya.
"Ina matukar kaunar Izoh. Na zuba lokacina da soyayyata. Na kuma tallafa mai da kudi saboda shi din dan buga-buga ne. Wasu lokutan ni zan biya kudin hayarmu harma da na abubuwan bukatunmu, amma ya rabu da ni bayan ya gama."

Rabuwansu ya yi illa sosai ga Nasha don har yanzu bata warke ba.

Nachi ta ce soyayya ba ta da kariya, amma tana kawo farin ciki

Matashiyar ta kuma bayyana cewa babu tabbacin samun kariya a soyayya.

Kara karanta wannan

“Manta Don Kin Ganni a Kan Babur”: Dan Najeriya Ya Tsara Budurwa a Kan Babur, Bidiyon Ya Yadu

Duk da halin da ta shiga a baya, Nachi ta yarda cewa soyayya na iya kawo farin ciki, koda dai tana dauke da hatsarurruka.

Ta ce:

"Ina ganin babu kariya a soyayya. Abun da ya faru da ni yana iya faruwa da kowa. Ba za ka iya samun kariya a so ba sannan don mugun abu ya faru, baya nufin zai kare cikin hawaye. Ba za ka tabbatarwa ba, amma za ka iya yanke hukunci na so da farin ciki a kodayaushe saboda so na kawo farin ciki masu yawa."

Kalli bidiyon a kasa:

Bayan hade asusun banki suna tara kudi da mijinta, mata ta fece da kudaden

A wani labarin kuma, wata matar aure ta yi nasarar yashe gaba daya kudin da ke cikin asusun hadin gwiwa nata da na mijinta.

Matar ta kuma yi batan dabo bayan ta kwashe kudin amma sai taki rashin sa'a domin dai an kama ta daga bisani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng