“Ina Da Kudi Fa, Manta Wai Kin Ganni a Kan Babur”: Matashi Ya Tsara Budurwa Kan Wani Mashi a Bidiyo

“Ina Da Kudi Fa, Manta Wai Kin Ganni a Kan Babur”: Matashi Ya Tsara Budurwa Kan Wani Mashi a Bidiyo

  • Yunkurin matashi dan Najeriyana tsara wata budurwa, wacce fasinja ce a kan wani babur ya ba mutane mamaki
  • Mutumin, wanda shima yake kan babur ya roki budurwar da ta bashi lambar wayanta sannan ta dauke tunaninta daga kan wai ta gansa a kan babur
  • Matashiyar ta juya baya inda ta kama dariya, amma hakan bai sanyayawa matashin gwiwa ba yayin da ya ci gaba da tsara ta

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani matashi dan Najeriya ya haddasa cece-kuce yayin da ya tsara wata kyakkyawar budurwa a kan babur da ke tafiya.

A wani bidiyo mai ban dariya da aka gano a TikTok, ya kira ta sannan ya gabatar da bukatarsa na cewa ta ba shi lambar wayarta.

Matashi ya tsara yar budurwa a kan mashin
“Ina Da Kudi Fa, Manta Wai Kin Ganni a Kan Mashin”: Matashi Ya Tsara Budurwa Kan Wani Mashi a Bidiyo Hoto: @keemlammi
Asali: TikTok

Matashiyar ta juya baya tana kallon mai son nata, wanda shima yana kan wani babur din ne, dauke da murmushi a fuskarta yayin da ta dauke kanta zuwa yadda yake da farko.

Kara karanta wannan

“Aiki Ya Yi Kyau”: Matashi Ya Kammala Hadadden Gidansa, Ya Zuba Kujeru Yan Waje Da Kayan Alatu

Ba tare da bata lokaci ba, matashin ya bukaci da ta manta cewa shi ma yana kan babur, inda ya kara da cewa motarsa ce ta samu matsala.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bidiyon ya ba jama'a mamaki.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

user3672321449376 ya ce:

"Ka badda kamanni a matsayin talaka don samun masoyi na gaskiya."

commentator ya ce:

"Baaba yarinyar na kyau fa."

user3672321449376 ya ce:

"Ka daina amfani da kudi don jan hankalin mata ba tushe mai kyau bane ga kowani soyayya.
"Idan kunne ya ji jiki ya tsira."

white fish ya ce:

"Ta ce tana biye da kai."

king Nelson Greenlight ya ce:

"Ba za ka iya ajiye mace da kudi ba ka yi kokari ka koyi wasan dan uwa."

Young:Escobar19986 ya ce:

"Na taba amfani da wannan dabarar na samu budurwa a baya."

Kara karanta wannan

Matashiya Ta Ajiye Girman Kai, Ta Isa Gaban Saurayinta Da Zobe Domin Neman Aurensa, Hotuna Sun Yadu

fresh ya ce:

"Me yasa dan achaban ke guduwa da ita, ka rage gudu yallabai."

Bayan hade asusun banki suna tara kudi da mijinta, mata ta fece da kudaden

A wani labarin kuma, wata matar aure ta yi nasarar yashe gaba daya kudin da ke cikin asusun hadin gwiwa nata da na mijinta.

Matar ta kuma yi batan dabo bayan ta kwashe kudin amma sai taki rashin sa'a domin dai an kama ta daga bisani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel