An Yi Sauye-Sauye Fiye da 20 a Gidan Soja, Hafsun Sojojin Kasa Ya Fara Rabon Mukamai
- Janar Taoreed Lagbaja ya fitar da wasu nade-naden mukaman farko da ya yi a ofishin COAS
- Jawabin sauyin da aka samu ya fito daga ofishin hulda da jama’a na sojoji, Onyema Nwachukwu
- Nwachukwu ya ce Laftanan Janar Lagbaja ya yi kira ga wadanda aka ba mukamai su zage dantse
Abuja - Shugaban hafsun sojojin kasa, Taoreed Lagbaja, ya amince da sababbin nadi da kuma wasu sauye-sauyen manyan jami’ai a fadin Najeriya.
Darektan hulda da jama’a na sojojin kasa, Onyema Nwachukwu ya sanar da wannan a wani jawabi. The Cable ta fitar da rahoto a yammacin Asabar.
Laftanan Janar Lagbaja yake cewa ya amince da canjin wasu manyan jami’an tsaro da ke bangarori da-dama ne saboda a ji dadin tafiyar da ayyuka.
Janar Lagbaja ya umarci wadanda su ka samu mukamai su kara kokarin wajen yakar kalubalen da ake fuskanta na ta’addanci da tada zaune-tsaye.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Su wa COAS ya tafi da su?
Kamar yadda jawabin na Onyema Nwachukwu ya nuna, nadin mukaman da aka yi sun kunshi:
1. AB Ibrahim — Sashen dabaru da tsare-tsare (DAPP)
2. BR Sinjen — Sashen ayyukan sojoji (DAOPs)
3. OR Aiyenigba — Sashen auna ayyukan sojoji
4. NC Ugbo — Sashen hulda da farar hula
5. E Akerejola — Sashen kai da komawa a Hedikwata
6. BA Alabi — GOC na Hedikwata ta I
7. AE Abubakar — GOC na Hedikwata ta 3/Kwamandan Operation Safe Haven (OPSH)
8. PP Mala — GOC na Hedikwata ta 7/Kwamandan bangaren dakarun Operation Hadin Kai (OPHK).
9. GU Chibuisi — Kwamandan bangaren dakarun Operation Hadin Kai (OPHK).
10. IS Ali — Kwamandan rundunar hadin gwiwa MNJTF
11. EAP Undiandeye — Shubaban leken asiri (NIA)
12. OO Oluyede — Kwamandan Sojojin yaki
13. MG Kangye — Kwamandan Sojojin da ke rike bindigogi
14. AA Adeyinka — Kwamadan sufuri a Hedikwata
15. KO Aligbe — Kwamdan horaswa
Rahoton ya ce sauran sojojin da su ka samu mukamai a nade-naden da aka yi su ne:
16. JO Ochai — Kwamandan makarantar NDA
17. IB Maina — Kwamandan makarantar ilmin yaki
18. TB Ugiagbe — Shugaban sashen leken asirin sojoji
19. OG Onubogu — Kwamandan cibiyar Martin Luther Agwai
20. N Ashinze — Darekta a sashen DIA
21. AO Onasanya — Shugaban sojojin fadar shugaban kasa
Rahoto ya zo cewa babu mamaki tsarin kasuwanci da na tattalin arzikin da Muhammadu Buhari ya kawo, su canza a gwamnatin Bola Tinubu.
Sabon shugaban Najeriya, Tinubu ya fara nuna yiwuwar inganta alaka da makwabta. A ‘yan shekarun bayan nan, gwamnatin tarayya ta rufe iyakokinta.
Asali: Legit.ng