Kotu Ta Yanke Wa Matashi Hukuncin Share Harabar EFCC Na Kwanaki 3 Bisa Zargin Damfara
- Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta umarci wani matashi da ya share harabar hukumar EFCC har na tsawon kwanaki uku
- Wanda ake zargin mai suna Okwo Mark ya yi shigan bultu tare da damfarar cewa shi jami'in hukumar FBI ne a Amurka
- Alkalin kotun, Aliyu Shafa ya umarci a daure Mark a gidan kaso har tsawon watanni uku ko biyan tara N50,000
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Wata kotu da ke zamanta a Abuja ta umarci matashi da share harabar hukumar EFCC na kwanaki uku bisa zargin damfara ta yanar gizo.
Hukumar EFCC ta kama Okwo Mark yayin da ya yi shigar bultu tare da bayyana kansa a matsayin Stella Coleman, ma'aikacin Hukumar Bincike ta FBI a Amurka.
Mark ya amince da aikata laifin da ake tuhumarsa, inda ya bukaci kotun ta masa sassauci.
Cire Tallafi: Kungiyar Ma’aikata Ta Bukaci FG Ta Kara Mafi Karancin Albashi Zuwa N200,000, Ta Yabi Wasu Jihohi
Alkali ya umarci Mark ya na zuwa ofishin EFCC don sharewa na kwanaki uku
Yayin yanke hukunci, Alkalin kotun, Aliyu Shafa ya daure Mark har tsawon watanni uku a gidan kaso ko biyan tara N50,000, Daily Nigerian ta tattaro.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Alkalin kotun ya kuma umarci matashin da ya share harabar hukumar EFCC har na tsawon kwanaki uku daga karfe 8:00 na safe zuwa 12:00 na rana.
Alkalin har ila yau, ya umarci a kona wayar da Mark ya yi amfani da ita tare da kawo shaidar tabbatar da kona wayar.
Lauyar Mark ta roki kotun ta yi wa matashin sassauci
Lauyan wanda ake zargi, B.E Danjuma ta fadawa kotu cewa Mark bai taba aikata wani laifi ba kuma ya yi dana sanin aikata laifin, cewar rahotanni.
A cewarta:
"Mark yaro ne dan shekara 21, kawai ya hadu ne da munanan abokai, bai taba aikata laifi ba, kuma ya yi dana sanin aikata wannan laifin.
"Tun da wannan shi ne karin farko na aikata laifin wanda ake zargin, muna rokon kotu da ta tausaya wurin yanke hukunci."
Kotu Ta Tasa Keyar Dan Damfara Zuwa Ofishin EFCC Don Karbar Lakca Na Mako 1
A wani labarin, kotu ta tura matashi mai suna Ndubuisi Success ofishin hukumar EFCC don karbar lakca.
Kotun ta ce matashin zai ke zuwa ofishin don karbar lakca ne har na tsawon mako guda daya.
A cewar kotun, hakan zai sa ya san amfanin damfara ko kuma rashin amfaninta ga al'umma.
Asali: Legit.ng